Abdollahian; Ziyarar Assad Ta Bude Wani Sabon Shafi Na Huldar Dake Tsakanin Iran Da Siriya.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian ya bayyana cewa ziyarar da shugaban kasar Syria Bashar al-Assad ya kawo birnin Tehran jiya Lahadi za ta bude wani sabon shafi na huldar dake tsakanin kasashen biyu.
Yayin da yake ishara da ziyarar da shugaban kasar Siriyar ya kawo Tehran da kuma ganawa da jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei da kuma shugaban kasar Ebrahim Raisi, Hossein Amir-Abdollahian ya bayyana cewa, ziyarar ta shugaba Assad tana da fa’ida.
A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Abdollahian ya ce ganawa tsakanin shugabanin kasasshen biyu za ta bude wani sabon babi na alaka mai inganci.
Ministan harkokin wajen Iran, ya kara da cewa, tsayin daka da Siriya ta yi ya haifar da sakamako mai kyau, kuma kasashen biyu sun kuduri aniyar daukaka dangantakar da ke tsakaninsu ta hanyar da ta dace da matsayin al’ummar Iran da Siriya.
READ MORE : Ivory Coast Na Karbar Taron Duniya Na COP-15 Kan Kare Muhalli.
Jiya Lahadi ne shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad ya kawo ziyarar ba zata a nan Tehran.
Marabin da ya ziyarci Iran, tun cikin watan Fabrairun 2019.