A Kalla Falasdinawa 32 Ne Su Ka Jikkata Sandaiyyar Harin Da Yan Sahayoniya Su Ka Kai Musu.
Kungiyar Agajin Falasdinawa ta “ Hilal-Ahmar” ta bayyana cewa; Falasdinawan sun sami raunuka ne a yayin taho mu gama da ‘yan sahayoniya a garin “ Burqah” da yake a Arewacin Nablus.
” Kungiyar agajin ta ci gaba da cewa; Tuni an dauki wadanda su ka fi samun raunuka masu tsanani zuwa asibiti domin yi musu magani.
Tun daga ranar juma’ar da ta gabata ne dai da yahudawan sahayoniya su ka fara kutse a cikin masallacin Quds, al’ummar Falasdinu su ka fito domin nuna kin amincewa.
Kwanaki uku a jere tun Lahadi, Litinin da jiya Talala ‘yan sahayoniyar su ke shiga cikin masallacin na Quds, a karkashin cikakkiyar kulawar ‘yan sanda.