APC za ta yanke shawara kan jadawalin zaben fitar da gwani.
Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya za ta yanke shawara kan jadawalin zabukanta na fitar da gwani a ranar Laraba.
Za ta dauki matakin ne a yayin taron majalisar zartarwarta, wanda shugabannin jam`iyyar suka ce zai mai da hankali ne wajen tattaunawa a kan shirin jam`iyyar na gudanar da zaben fid da gwani domin tunkarar babban zaben 2023.
Wannan shi ne karon farko da kwamitin zartarwar APC zai yi zama bayan babban taron jam`iyyar, inda aka zabi sabbin shugabanni na kasa.
Kazalika taron ya zo ne a lokacin da hukumar zabe ta bai wa jam`iyyun siyasa wa`adin nan da watan Yuni mai zuwa su mika mata sunayen wadanda za su yi takara da tutocinsu.
Daraktan yada labarai na jam`iyyar APC, Mallam Salisu Na`inna Danbatta, ya shaida wa BBC cewa “idan Allah ya yarda a zaman da za a yi, za a duba tsarin da aka yi na shirye-shiryen yin zabuka na cikin-gida da kuma yadda jam’iyyar za ta cika dokokin hukumar zabe na shiga babban zaben da za a yi a shekara mai zuwa.”
Ya kara da cewa baya ga batun jadawalin zabukan fitar da gwani, jam’iyyar ta APC za ta tattauna kan wasu batutuwa da suka “shafi ita jam’iyyar APC da ‘ya’yanta da nasarorin da ake hange za ta kara samu nan gaba.”
Duk da cewa jam`iyyar APC ba ta fayyace sauran muhimman batutuwan da suka shafi `ya`yan nata ba, wani abu da ya fito fili, wanda kuma ya fara fusata wasu `yan jam`iyyar shi ne zargin rashin adalci da suka cewa ana yi a jam`iyyar.
Tuni wasu jiga-jigan jam`iyyar suka sauya sheka ko kuma suka kama hanyar yin hijira daga jam`iyyar APC irin su tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari da Sanata Kabiru Marafa da ma wasu jiga-jigan jam’iyyar.
Sanata Kabiru Marafa ya shaida wa BBC cewa jam’iyyun siyasa da dama ne ke zawarcinsu, bayan zaluncin da yake zargin APC ta yi masu.
Sanatan ya shaida wa BBC cewa “Gaskiya jam’iyyu da yawa sun nemi mu suna son mu taka karagar motarsu domin kai wa ga biyan bukatu na siyasa.”
Barrister Soloman Dalong, tsohon Ministan Wasanni, kuma dan ga-ni-kashe-nin jam`iyyar APC, ya ce shi da APC haihata-haihata, har ma ya samu masuki a jam`iyyar SDP.