Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya amince da fitar da Naira biliyan 1.3 a matsayin tallafin karatu ga daliban aikin jinya da unguwar zoma 997 daga jihar.
Zulum ya amince da fitar da kudin ne a yayin da ya bayyana haka a ranar Laraba yayin da yake kaddamar da shirin bayar da tallafin karatu a kwalejin koyon aikin jinya da unguwar zoma da ke Maiduguri.
Ya ce, daga cikin sunayen mutane 1,080, 40 daga kowace karamar hukuma 27 na jihar, 997 ne suka cancanci cin gajiyar tallafin.
Ya kuma bayyana cewa, dalibai 997 da suka ci gajiyar tallafin, za a basu takardar kama aiki da zarar sun kammala karatun.
Gwamnan ya ce, tallafin da aka bayar, an yi ne don karfafa wa daliban kwarin gwiwar kammala karatunsu ta yadda za a cike gibin gurbin ma’aikata a tsarin kiwon lafiya na jihar.
A wani labarin na daban gwamnan jihar Adamawa Ahamdu Umaru Fintiri, ya nuna damuwa game da karuwar ayyukan yara ‘yan shila a Yola, babban birnin jihar, inda ya dora alhakin matsalar kan iyayen yaran.
Da take magana a madadin gwamnan, mataimakiyar gwamnan jihar Farfesa Kaletapwa Farauta, ta ce kamata yayi iyaye su sa ido kan harkokin yaransu na yau da kullum, domin nauyi ne da Allah zai tambayesu a ranar gobe.
Ta ci gaba da cewa “a madadin gwamna Ahamdu Umaru Fintiri, muna rokon iyayen yara da su rika tura yaransu cibiyoyin koyon sana’o’in dogaro da kai, da zai taimakawa yaran su samu sana’ar da za su dogara da kansu kuma su samu tallafin gwamnatin bayan sun koyi sana’ar da ransu yake so.
“Haka ya kamata, maimakon su rika aikata munanan yyukan da wata rana zai kaisu ga rasa rayukansu, bai Kamata ba, iyaye su gargadi yaransu domin su ne shugabannin gobe” inji Farauta.
DUBA NAN: Kiraye Kirayen Gwamnonin Kano Da Kebbi A Bikin Sallah
A nasa jawabin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, SP Suleiman Yahya Nguroji, ya ce, rundunar ta dauki tsauraran matakai kan yaran inda ya ce, rundunar ta kame yara ‘yan Shila fiye da 100, ta kuma gurfanar da su a gaban kotu.