Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP a 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi gwamnatin tarayya da jam’iyyar APC da daukar matakan da ba su dace a kan sha’anin harkokin Kano ba.
Kwankwaso, ya bayyana zargi din ne a wajen kaddamar da aikin titin Madobi mai tsawon kilomita 82 a garin Madobi.
Tsohon gwamnan na Kano, kuma jagoran gwamnatin jihar, ya bayyana cewa al’ummar Kano ba za su lamunci duk wani yunkuri na katsa-landan a sabgar da ta shafi jiharsu ba.
Ya kuma jaddada aniyar ‘yan Jihar Kano na mara wa gwamnanatin Kano baya duk da tsoma bakin da gwamnatin tarayya ke yi.
Kwankwaso, yayin da yake jawabi ga wadanda ya bayyana a matsayin makiyan jihar, ya soki gwamnatin tarayya da daukar tsauraran matakai, kamar son kafa dokar ta-baci a Kano da sauransu wajen hana Jihar ci gaba.
Kwankwaso ya shawarci gwamnatin tarayya da ta yi hattara da ’yan siyasa marasa kishin kasa daga Kano, yana mai gargadin cewa irin wannan kawancen ba zai haifar da ɗa mai ido ba.
A wani labarin na daban shugaba Bola Tinubu ya taya al’ummar Musulmi murnar sallah babba, inda ya bayyana muhimmancin sadaukarwa da hadin kai a tsakanin al’ummr kasar nan.
Ya yi fatan Allah Ya karbi addu’o’in da Musulmi suka yi a ranar Hajji.
Shugaba Tinubu ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi la’akari da muhimmancin sadaukarwa da aiki wajen gina kasa.
Shugaban ya kuma amince da irin sadaukarwar da ‘yan Nijeriya suka yi a shekarar da ta gabata.
Ya bayar da tabbacin cewa hakurin da al’umma suka yi zai haifar da sakamako mai kyau, tare da bunkasa tattalin arzikin kasar nan.
A karshe, shugaba Tinubu ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta samar da tsaro, gyara zamantakewa, da tattalin arzikin dukkanin ‘yan Nijeriya.
Ya bukaci al’ummar kasar nan da su ci gaba da yin addu’o’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali domin samun ci gaban da ake muradi.