‘Yan bindiga a Najeriya sun kwashe akalla mutane 50 da suka halarci bikin aure a Sokoto lokacin da suke komawa Gusau ta Jihar Zamfara a karshen makon nan.
Shaidun gani da ido sun ce da yammacin jiya ne ‘Yan bindigar suka tare hanyar lokacin da masu bikin ke komawa gida, inda suka bude wuta akan daya daga cikin motocin dake cikin tawagar su abinda ya tilasta musu tsayawa.
Rahotanni sun ce tawagar masu bikin ta fito ne daga Tambuwal lokacin da take komawa Gusau babban birnin jihar zamfara, kuma nan take Yan bindigar suka kwashe matafiyan suka gudu da su cikin daji.
‘Yankin arewa maso yammacin Najeriya na ci gaba da fuskantar hare haren ‘Yan bindiga wadanda ke kashe matafiya da mazauna karkara tare da garkuwa da wasu domin karbar diyya.
A wani labarin na daban mazauna kauyukan karamar hukumar Bakura dake Jihar Zamfara a Najeriya na zaman makoki sakamakon kisan gillar da Yan bindiga suka yiwa mutane sama da 50 a wani kazamin hari da suka kai musu a karshen mako.
Rahotanni sun ce ‘Yan bindigar sun tsara yadda suka mamaye kauyukan guda 3 da suka hada da Sabon Garin Damri da Kalahe, inda suka bude wuta akan mai uwa da wabi.
Yan bindigar sun afkawa asibiti garin Damri,inda suka kashe masu jinya tareda kona motar yan Sanda .Da samun labarin wannan hari,an tura sojoji,wandada suka samu nasarar korar yan bindigar.
Jihar Zamfara na ci gaba da fama da matsalar tsaro sakamakon hare haren Yan bindiga wanda ya kaiga rasa dubban rayuka a kaasr.