Zainab Matar Ahmad Usman, dan banga da aka yi kashe a Lugbe Abuja kan zargin yi wa Annabi batanci ta ce sharri aka yi wa mijinta.
A hirar da aka yi da ita, Zainab wanda ke dauke da juna biyu na tsohon mijin ta kuma ce mahaddacin Alkur’ani ne shi sannan tana zargin an kashe shi ne saboda jajircewarsa kan aiki.
Ta ce ba za ta yafe wa wadanda suka kashe mata mijinta ba sai dai tana addu’a Allah ya shiryi masu hali na daukan doka a hannu ba tare da tabbatar da huja ba.
Zainab, matar ma’aikacin sintiri Ahmad Usman wanda aka kashe shi a unguwar Lugbe, Abuja kan zargin yin batanci ga Manzon Allah (SAW) ta ce mijinta mahhadacin Alkur’ani ne kuma sharri aka masa. An Kashe Min Mijina Musulmi Mahaddacin Alkur’ani Kan Zargin Zagin Annabi, In Ji Zainab.
Ta bayyana hakan ne cikin hirar BBC Hausa ta yi da ita yayin ziyarar da wakilin ta ya kai gidansu marigayi Ahmad.
Rahoton ya nuna Zainab tana takaba kuma tana dauke da juna biyu. Sharri aka yi wa Ahmad, In ji Zainab Zainab wanda rahoton ya ce har yanzu tana cikin damuwa da juyayin rashin mijinta ta ce kazafi aka masa hakan yasa abin ya fi damunta a zuciya.
“A kodayaushe mijina ba shi da wata magana sai dai ka ji ya ce ‘mu yi wa Annabi salati’ kuma ya haddace Alkur’ani a kansa,” in ji ta.
Ta dage cewa babu yadda za a yi mijin nata ya yi wa Annabi batanci. Ta ce ba za ta yafe wa wadanda suka kashe mata miji ba – amma ta roki Allah ya shirya masu irin wannan halin na daukar doka a hannunsu ba tare da hujja ba.
“Jajircewarsa a kan aiki ne yasa aka yi masa ‘sharri’ kuma har ta kai ga halaka shi,” in ji matar mai cewa biyu.
Zainab ta ce tun tana jaririya iyayenta suka rasu don haka tana daukar mijinta a matsayin ‘uwa da uba’ saboda yana tausayinta kuma yana share mata hawaye.
Source:hausalegitng