Zaɓen 2023; TMG ta gargaɗi masu rike da mukaman gwamnati a Najeriya kan amfani da dukiyar al’umma a yaƙin-zaɓe.
Ƙungiyar da ke sa-ido kan harkokin zaɓe a Najeriya wato TMG, ta gargaɗi masu riƙe da muƙaman gwamnati a kan amfani da dukiyar ƙasa wajen gudanar da yaƙin neman zaɓe da sauran harkokin jam’iyya.
Ƙungiyar ta ce ta lura da yadda wasu manyan jami’ai, ciki har da ministoci, suke amfani da kayan gwamnati kamar jiragen sama da motoci, har ma da kuɗaɗe wajen yin kamfen.
Shugaban ƙungiyar, Auwal Musa Rafsanjani, ya shaida wa BBC cewa abu ne da ba za a lamunta da shi ba, kuma ya yi ikirarin cewa a gwamnantin Muhammadu Buhari ce kadai aka samu irin wannan karya doka.
Ya kuma nuna damuwa a kan makudan kudaden da masu rike da mukaman gwamnati suka kashe wajen sayan fom din tsayawa takara.
“Fom-fom da suka saya, a ina suka nuna kadarorin da suka mallaka kafin su hau, da har suke facaka irin wannan saboda an san ko nawa kake dauka kuma a baya ba ka fada kana da irin wadannan makudan kudaden ba,” in ji shi.
TMG ta ce akwai dokar kasa da ta haramta wa masu rike da mukaman gwamnati kamfe ko nuna sha’awar tsayawa takara, kuma ta ce dole su yi murabus idan za su yi.
Kungiyar ta ce a baya wadanda suka rike mukaman gwamnati sun yi murabus a lokacin da suka bayyana anniyarsu ta tsayawa takara.
Rafsanjani ya ce wannan wata alama ce da ke nuna cewa yaƙi da cin hancin da rashawa da ake yi a Najeriya ya tsaya ne kawai a fatar-baka.
Duk da cewa an samu wasu ‘yan Najeriya da suka kalubalanci dokar da ta hana su tsayawa takara a gaban kotu, kungiyar TMG ta ce Majalisar Dokoki ce take yin doka don haka ya zaman wajibi a mutunta dokar.
“Majalisa ta yi doka kuma shugaban kasa ya rattaba hannu akai duk wanda ya ce bai yadda da dokar ba, sai ya je majalisa, domin ta yi kwaskarima ba maganar zuwa kotu ba ce,” a cewar Rafsanjani.
Rahotanni dai na cewa kawo yanzu akwai jami’an gwamnati da dama, ciki har da ministoci biyar, da suka nuna anniyar tsayawa takarar shugaban kasa a zaɓen 2023 ba tare da sun ajiye mukamansu ba.