Wasu tsagerun yan bindiga sun farmaki gidan ɗan takarar gwamnan jihar Osun na jam’iyyar Labour Party (LP), Yusuf Lasun.
Bayanai sun nuna cewa maharan sun buɗe wuta a gidan, babu wanda ya jikkata amma sun farfasa gilasan gidan Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Osun, Yemisi Opalola, ya tabbatar da harin, ya ce sun gode Allah babu wanda ya ji rauni.
Da safiyar nan ta Litinin, wasu miyagun ‘yan bindiga sun kai hari gidan Yusuf Lasun, ɗan takarar gwamna na jam’iyyar Labour Party a zaɓen jihar Osun.
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa ƴan bindigan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare, farkon safiyar Litinin a gidan ɗan siyasar da ke Ilobu, ƙaramar hukumar Irepodun.
Rahotanni sun nuna cewa ba bu wanda ya jikkata yayin harin amma maharan sun yi wa gidan ɓarna yayin da suka buɗe wuta.
Harin da aka kai gidan Mista Lasun, tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin tarayya, awanni bayan ya fafata a muhawarar ‘yan takarar gwamna da ya gudana a Osogbo.
A wurin muhawarar, Yusuf Lasun, ya fuskanci gwamnan Osun na APC, Gboyega Oyetola, Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP, Oyegoke Omigbodun na jam’iyyar SDP da Akin Ogunbiyi na Accord Party.
Mista Lasun ya ɗora laifin rashin tsaro da ya addabi jihar da mafi yawan sassan Najeriya kan gwamnati kuma ya yi kira da a samar da yan sandan jihohi.
A ranar 16 watan Yuli, 2022, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC zata gudanar da zaɓen gwamnan jihar Osun.
“Ina tunanin hakan ta faru ne saboda muhawarar da aka gudanar jiya, saboda ana kammala wa labari ya canza a jihar Osun.”
“Wannan ba shi ne karo na farko ba, an taɓa kai masa hari a kwanakin baya, an kai hari Ofishinsa watanni kaɗan da suka gabata kuma ko a wancan lokacin ba mu wani tada hankali ba saboda mutanen Osun sun san abinda ke faruwa.”