Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC, sun janye yajin aikin da suka fara a fadin kasar nan.
Wata majiya mai tushe daga NLC ya shaida wa LEADERSHIP cewa kungiyar kwadago ta dage yajin aikin ne na ‘yan kwanaki.
Ayyukan masana’antu da harkokin tattalin arziki da gwamnati sun durkushe a fadin kasar nan bayan fara yajin aikin da kwana biyu.
Kungiyar kwadago ta dakatar da yajin aikin ne, bayan taron majalisar zartarwa na kasa (NEC), da suka yi a Abuja a ranar Talata.
Kungiyar ta cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayya kan sabon mafi karancin albashi a ranar Litinin.
A wani labarin na daban jragen yakin saman Operation Whirl Punch da Operation Hadarin Daji sun lalata sansanin ‘yan ta’adda a Jihohin Kaduna da Katsina.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Air Vice Marshal Edward Gakwet, cikin wata sanarwa, ya ce an kashe ‘yan ta’adda da dama a hare-haren jirgin yaki ta sama da suka kai.
A cewar AVM Gabkwet, ya ce dakarun sun kai hare-hare ta sama a Buharinyadi, da ke yankin dajin Bula a karamar hukumar Giwa ta Jihar Kaduna tsakanin 30 zuwa 31 watan Mayu, 2024.
Ya ce binciken da suka yi sun gano ‘yan ta’adda dauke da makamai da ke yawo cikin wasu bukkoki da kuma babura sama da 13.
Kakakin, ya kara da cewa, majiyoyi da dama sun bayyana cewa ‘yan ta’addan ne ke da alhakin kai hare-hare da garkuwa da mutane a wasu yankuna na karamar hukumar Birnin Gwari da Igabi da kuma Giwa.
Daraktan ya ce rundunar ta sake kai wasu hare-hare ta sama a ranar 2 ga watan Yuni, 2024, inda suka lalata sansanin kasurgumin dan ta’adda Alhaji Iliya da yaransa a tsaunin Zango da ke karamar hukumar Kankara a Jihar Katsina.
Ya ce “bayan kai harin, hotunan sun nuna yadda aka yi nasarar kawar da ‘yan ta’adda da dama a yankin”.
DUBA NAN: Alkalin Alkalan Najeriya Ya Kira Alkalai Guda Biyu Da Sukayi Shari’ar Masarautu A Kano
Ya bayar da tabbacin cewar za su ci gaba da kai hare-hare don kawar da ‘yan ta’adda da kuma wanzar da zaman lafiya a yankunan.