Har yanzu tsugune ba ta kare ba tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago (NLC), yayin da suka amince da ci gaba da tattaunawa kan batun cire tallafin mai kafin wa’adin kwanaki 21 da kungiyar ta bayar na shiga yajin aikin sai baba ta gani.
Dukkansu sun yi alkawarin samar da mafita ga muhimman bukatun a lokacin zaman tattauwan kafin wa’adin ya cike.
Ministan kwadago da samar da aiki, Mista Simon Lalong ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen wata ganawar sirri da kungiyar NLC a Abuja.
Ministan ya kira taron ne domin dakile yajin aikin da kungiyar kwadago ta shirya yi da sauran batutuwa.
Idan dai za a iya tunawa, kungiyar NLC ta yi barazanar fara yajin aikin daga ranar 21 ga watan Satumba, saboda halin kuncin da talakawa ke ciki sakamakon cire tallafin man fetur.
A cewarsa, “Mun yi tattaunawa mai ma’ana a kan abubuwa da dama da NLC ta gabatar wa gwamnatin tarayya a baya.
“Yawancin abubuwan da kungiyar ta gabatar har yanzu ana la’akari da su kafin yanke hukunci na karshe,” in ji shi.
Sai dai ministan ya ce gwamnatin tarayya na kokarin magance matsalolin ma’aikata kamar yadda NLC ta gabatar.
Shugaban kungiyar NLC, Mista Joe Ajaero ya ce bangarorin biyu sun amince su ci gaba da tattaunawa don cimma yarjejeniya mai ma’ana kafin wa’adin ya kare.
Ya kara da cewa, duk lokacin da aka gayyace su za su kasance a wurin. Ya ce bangarorin biyu za su yi aiki don cimma matsaya kafin kafin karshen lokacin wa’adin.
Source: LEADERSHIPHAUSA