Hukumar jin dadin alhazai ta kasa, NAHCON ta bayyana cewa za’a kammala jigilar Alhazan bana (2024) zuwa kasar Saudiyya a ranar 10 ga watan Yuni ko kuma kafin ranar.
Mataimakiyar daraktar hulda da jama’a ta NAHCON, Fatima Saada Usara ce ta bayyana hakan, inda ta kara da cewa, an kaddamar da jigilar Maniyyatan Nijeriya ne na bana a jihar Kebbi ranar Laraba, sannan kuma jirage biyu za su tashi dauke da maniyyatan jihar Nasarawa da babban birnin tarayya (FCT) a filin jirgin sama na Abuja.
Ta kara da cewa, Jirage biyu za su ci gaba da tashi a kowace rana daga bisani kuma a kara ya zama biyar a kowacce rana.
Usara ta kara bayyana cewa, an kebe filayen jiragen sama 15 don gudanar da aikin Hajjin 2024 tare da mahajjata 65,047 daga bangaren gwamnati da masu zaman kansu.
“Jami’an diflomasiyya, ma’aikatan Hukumar aikin hajji tare da mataimakin shugaban kasa, Mai girma Kashim Shettima ne, suka halarci taron kaddamar da jirgin farko na mahajjatan bana (2024),” in ji ta.
A wani labarin na daban jam’iyyar Tarayya da ke Birnin Kebbi, FUBK ta gudanar da bikin daukar dalibai 2,217 da za su yi karatun digiri na farko da na biyu a Fanni daban-daban, a harabar jami’ar da ke Unguwar jaji a karamar hukumar Kalgo a Jihar.
An kafa jami’ar ne a cikin shekarar 2013 kuma ta fara karatu tare da dalibai a cikin shekarar 2014 inda take da sashin digiri 24, ya zuwa yanzu tana da sashin karatun digiri 37 da sashin karatun gaba da digiri na farko guda 20.
A nasa jawabin, Shugaban jami’ar Farfesa Zayyan Muhammad Umar ya bayyana cewa, jami’ar a shirye take ta yi amfani da kudadenta tare da karfafa ribar da take samu a halin yanzu domin bude sabbin hanyoyin samun dama ga ma’aikatanta da dalibanta.
Wannan bikin taron daukar Dalibai da jami’ar ta yi dai, shi ne karo na 9 tun bayan kaddamar da Jami’ar a shekarar 2013.
“Jami’ar ta karbi bukatar dalibai 2,530 da suka nemi gurabun karatun digiri na farko a jami’ar a wannan zango, an bai wa dalibai 2,269 damar yin rajista amma 2,095 ne kadai suka yi nasarar samun gurbin karatu.
DUBA NAN: Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Tashar Jirgin Ruwan Ta Tudu
“A matakin digiri na biyu, an samu jimillar Dalibai 112 da suka nema, kuma duk suna ci gaba da karatunsu a halin yanzu.” inji shi.