A wannan makon ne gamayyar kungiyoyin kwadago (NLC) da kungiyar kasuwanci (TUC) suka janye shirinsu na tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga da suka shirya za su yi.
Wannan matakin janyewar ya zo ne, bayan wata doguwar tattaunawa tsakanin wakilan kungiyoyin da wakilan gwamnatin tarayya, yanzu dai bangarorin biyun sun cimma matsaya wadda ta kai da dakatar da tsunduma yajin aikin da kwana 30 masu zuwa.
Idan za a iya tunawa kungiyoyin sun yi shirin shiga yajin aikin ne saboda matsin rayuwa da mafi yawan ‘yan Nijeriya suke ciki, wadanda suka samo asali sakamakon cire tallafin man fetur da wasu sabbin manufofi da gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu take aiwatar da su.
Wasu daga cikin abubuwan da aka cimma akwai karin albashi na naira 35,000 da gwamnatin tarayya ta amince za ta bayar ga dukkanin ma’aikatanta, wanda za a fara daga watan Satumbar da ya gabata, kafin a samu matsaya kan sabon mafi karancin albashi wanda ake tsammanin za a mayar da shi doka.
Sannan kuma gwamnatin tarayya ta dakatar da karbar harajin kan man dizel nan da wata shida masu zuwa. Haka kuma akwai maganar motocin sufuri masu amfani da gas da ake sa ran gwamnatin za ta kawo nan ba da jimawa ba don a sami sauyi daga amfani da man fetur.
Batun biyan albashin malaman gaba da sakandire na gwamnatin tarayya da ke bin bashi, wanda shi ma an mika shi gaban ma’aikatar kwadago da ayyukan yi domin ci gaba da duba shi.
“Sanya naira biliyan 100 don sayo manyan motocin bas-bas masu amfani da man gas don saukaka wa jama’a kan hanyar zirga-zirga a duk fadin kasar nan, wanda ake sa ran za a yi a watan Nuwamba mai zuwa.
Sannan kuma an cimma yarjejeniyar cire haraji ga wasu kamfanoni da daidaikun jama’a don saukaka masu wajen hada-hadar yau da kullum.
Bugu da kari, an cimma yarjejeniyar sasantawa da kungiyar direbobi ta kasa (NURTW) tare da sanya baki a batun fara biyan naira 25,000 a duk wata daga Oktoba ga ‘yan Nijeriya mutum miliyan15, wanda ya hada da tsofaffin ma’aikata masu karbar fansho.
Akwai kuma kara fadada shirin nan na rabon taki ga manoma a duk fadin kasar nan. Haka kuma an amince da cewa su ma jihohi da kananan hukumomi za a karfafa masu gwiwa domin aiwatar da wannan karin albashi ga ma’aikatan su.
Za a samar da kudade ga matsakaita da kananan masana’antu, sannan za a mayar da hankali wajen kirkiro da ayyuka ga matasa. Sannan kuma a fito da shirin zagaya matatun man fetur din kasar nan don tantance irin gyaran da suke bukata.
Wani abu kuma shi ne, gwamnatin tarayya za ta yi amfani da takardun da kotu ta sahale ne wajen saka hannu a kan wannan yarjejeniyar fahimtar juna cikin mako daya.
Ita dai wannan yarjejeniya ta samu sanya hannun shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero da sakataren kungiyar, Emmanuel Ugboaja da shugaban kungiyar TUC, Festus Osifo da sakataren kungiyar, Nuhu A. Toro
A bangaren gwamnatin tarayya kuwa, akwai ministan kwadago, Simon Bako Lalong da karamin ministansa, Nkeiruka Onyejeocha da kuma ministan yada labarai, Alhaji Mohammed Idris.
Wannan lamari na yajin aikin kungiyar kwadago ya tayar da kura a cikin kasar nan, wanda ‘yan Nijeriya suke ta bayyana ra’ayoyinsu kan lamarin.
Source LEADERSHIPHAUSA