A Jiya ne a abuja babban birnin tarayya shugaba muhammadu buhari ya bukaci likitoci dasu kaucewa tsunduma yaji aiki domin hakan ba farar dabara bace kuma bazai haifar da da mai ido ba duba da yanayi matsi da ake ciki a dai dai wanna lokaci.
Buhari ya bukaci likitocin maimakon su tsunduma yajin aiki zaifi alfanu su cigaba da gudanar da ayyukan su sa’annan su zabi zama su tattauna da gwamnati domin warware matsalolin da suke koke a kansu koda kuwa hakan zai dauki lokaci mai tsawo, kamar yadda shugaba buharin ya bukata.
Rayuwar wadanda zata shiga hadari idan likitoci suka tsunduma yajin aikin ya isa a tabbatar an bi hanyoyin sulhu da tattaunawa domin tabbatar da cewa ba’a tsunduma yajin aikin ba, a ta bakin buhari lokacin daya karbi bakuncin kungiyar likitoci ta najeriya a fadar mulki dake babban birnin tarayyar Abuja.
Buhari a ta bakin mai bashi shawara kan lamurran yada labarai Garba Shehu ya bayyana cewa duk kudaden da likitocin suke bin gwamnati za’a biya su bayan an gama tantancewa amma dai bai kamata a shiga yajin aiki a irin wannan mawuyacin hali da kasa take ciki ba.
Buhari ya jaddada cewa tabbatar da walwala da lafiyar al’umma baya takaita ga gwamnati kadai bane a’a ya shafi kowa da kowa musamman masu ayyukan kwararru irin likotoci da lauyoyi, bari nayi magana kai tsaye da likitoci masu ra’ayin tafiya yajin aiki ku sani lallai tafiya yajin aiki a wanna n lokaci bamafita bace saboda haka ku canja ra’ayi, inji shugaba buhari.
Shugaba buhari yayi nuni da cewa gwamantin sa tana iya kokarin ta domin tabbatar da fita hakkin ma’aikata da kuma ‘yan fansho wanda ciki har da ma’aikatan lafiya.
Yace na duba bukatun ku kuma naga ma tuni mun cika guda 12 daga ciki, sai dai bincike ya tabbatar da cewa harkar lafiya ta matukar samun ci baya a mulkin shugaba buharin wanda haka ne ma ya tilsata ma likitocin barazanar shiga yajin aiki idan gwamnati bata biya mata bukatun data zana ba.