Wasu Tsoffin kansisloli ne suka taru sukaiwa gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje addu’ar alquniti.
Kansilolin sunyiwa gwamnan Alqunuti ne sabida danne musu hakkinsu da suke zargin yayi.
Cikin wasu kansilolin sun rasa ransu sabida kin biyansu hakkinsu da akayi kaman yadda daya daga cikin tsoffin kansilolin ya fada.
Tsoffin kansiloli a sama da 360 sun gudanar da taron addu’ar alqunuti kan Allah yasa gwamnatin jihar kano ta biyasu hakkokinsu da suke bi.
Tsoffin kansilolin da yawansu sun hadiyi zuciya sun mutu sabida kunci da bakin cikin rayuwar da gwamnatin Gandujen ta yi musu.
A yayin da suke zantawa da gidan radion Freedom a cikin shirin inda ranka sun ce: “Mun zo kan gwamnati kano ta tausaya mana ta biyu mu hakkokinsu wanda idan an biya mu zamu samu saukin rayuwa.”
“A taimaka mana a dube mu, duk wanda ya gan mu ya san muna cikin yanayi.”
“Mun yi kansila mun hidimtawa wa al’umma, mun sauka an bar mu a cikin wani yanayi, yau sati na guda rabona da gidana, in ji wani da cikin su.
Muna sane da su, Gwamnati Amma da Freedom Radio ta tuntubi ma’aikatar kananan hukumomin jihar kano, ta bakin kwamishinan ma’aikatar Lamin Sani, yace suna sane da hakkokin tsoffin kansilolin suke bi, amma yace yawancinsu tun lokacin gwamnatocin baya ne.
“Amma ya ce gwamnatin jihar na bi daki-daki wajen biyan su hakkokinsu da suke bi. ”
Muna yin duk mai yiwa ganin mun biya su hakokinsu da suke bi” inji Lamin Sani Amma Kwamishinan ya bukaci kansilolin kan su kara hakuri kan hakkokin nasu.