Wata tawagar masu Tattakin Arba’in sun taso daga kudancin kasar Iraki, suna masu tafiya Karbala daga Garin Ras al-Bisheh da Bandar Faw.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – ya habarta cewa, Masu tattakin a kan wannan hanya suna wucewa ta cikin hanyar Bandar Faw mai ruwa da fadama na tsawon sa’o’i; A jiya ne wasu gungun wadannan maziyarta suna gudanar da alhinin shahadar shahidan Karbala a yayin da suke rike da tutoci da aka kawata da sunan Imam Hussain (amincin Allah ya tabbata a gareshi)
Maziyartan Arbaeen Husseini a birnin Ras al-Bisheh suna ci gaba da gudanarbda tattakin nuna alhini na tsawon sa’o’i da dama, bayan haka kuma wasu tsirarun mutane sama da 50 sun ci gaba da tafiya tare da daga sautin Labbaik Ya Hussain.