Tankar dakon man fetur ta yi bindiga kuma nan take ta kama da wuta a jihar Ondo ranar Litinin 6 ga watan Janairu, 2023.
Wani da lamarin ya faru a gabansa ya shaida wa yan jarida cewa Tankar na kokarin sauke mai kuma matsin lamba ya jawo haɗarin.
Bayanai sun nuna cewa karo na farko kenan da Tankar ta fara aiki bayan ɓare ta sabuwa, mutane sun shiga tashin hankali.
Wata babbar Tanka ta dakon man Fetur da ke aikin raba mai a gidan sayar da Man Fetur ‘Optimal Petrol Station’ a jihar Ondo, ta fashe sannan ta kama da wuta.
Jaridar Punch ta tattaro cewa Babbar Tankar ta kone ƙurmus sakamakon haɗarin kuma wutar da ta kama ta taɓa wani sashin gidan Man.
Wani ganau, Emmanuel Solomon, wanda abun ya faru a gabansa ya shaida wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne sanadin matsawa Tankar har ta yi bindiga kana wuta ta kama ci.
Bayanai sun nuna cewa mazauna yankin sun tsorata da faruwar lamarin kana suka fara harhaɗa kayansu jakunkuna domin jiran abinda ka iya zuwa ya komo.
A rahoton The Nation, kawo ɗaukin gaggawa da jami’an hukumar kashe gobara na ƙasa da hukumar kwana-kwana ta jihar Ondo suka yi ya taimaka matuka wurin kashe wutar.
Haka zalika wasu bayanai sun nuna cewa Tankar da ta fashe ɗin sabuwa ce kuma wannan shi ne lokaci na farko da zata kai Man Fetur.
Wannan matsala na zuwa ne a daidai lokacin d aake fama da karancin man Fetur a wasu yankunan kuma ‘yan Najeriya na shan mai da tsada.
Lamarin dai ya jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin kakanikayi da wahalar layin mai a gidajen mai yayin da ya rage ‘yan.makonni a fita zaben shugaban ƙasa.
Dan Allah Ku Yafe Mun, Tinubu Zai Dora Daga Inda Na Tsaya, Buhari
A wani labarin kuma Shugaba Buhari ya haɗa da Allah, ya roki ‘yan Najeriya su ƙara hakuri kuma su yafe wa gwamnatinsa.
Yayin ralin APC a jihar Katsina ranar Litinin, Buhari ya ce Tinubu zai gyara kuskuren gwamnatinsa ya ɗora daga inda ya tsaya.
Shugaba Buhari ya kuma dora laifin halin da ake ciki kan farfaɗiyar tattalin arziki sakamakon annobar cutar Korona Birus.