A halin da ake ciki a Nijeriya batun janye tallafin mai na ci gaba da zama babban abin damuwa ga al’ummar kasa musamman ganin yadda cire tallafin ya janyo mummunar dagulewar walwalar jama’a da kara matsatsi kan halin rayuwa gami da tsadar kayan amfani a kasar.
Wannan batun na ci gaba da daukan hankalin jama’a yayin da gwamnatoci ke ikirarin nemo hanyoyin shawo kan matsalolin da ake ciki.
A wani matakin da ke kara jefa wa ‘yan Nijeriya ayar tambaya shi ne yadda gwammatin tarayya karkashin Bola Tinubu ta fara yunkurin kinkimo basuka ba ya ga tulin bashin da gwamnati baya ta gadar wa kasar.
A watan Yulin 2023 gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gabatar da bukatar neman bashin dala miliyan $800 daga bankin duniya domin gudanar da shirin kyautata walwala da jin dadin rayuwar al’umman kasa.
Wannan yunkurin dai an yi ne domin rage radadin wahalhalun da cire tallafin man fetur ya haddasa, inda shugaban ya nemi majalisar dokoki ta amince da karbo bashin dala miliyan 800.
Tinubu ya ce za a ba da N8,000 ga gida miliyan 12 duk wata daga bashin da za a karbo daga Bankin Duniya.
Sai dai hakan ya janyo sukar lamirin daga bangarori da dama kuma daga bisani Shugaba Tinubu ya ba da umarni cikin gaggawa a sake nazari kan tallafin N8,000 da aka yi niyyar bai wa ‘yan Nijeriya.
Mutane da dama da muka zanta da su, sun soki lamarin tare da cewa wannan kudin ba zai yi komai wajen cire jama’a daga mawuyacin halin da suke ciki ba.
A makon jiya bayanai sun karade wasu kafafe inda aka yi zargin cewa gwammatin tarayya ta dawo da biyan tallafin mai a boye duk kuwa da cewa ya sanya hannu kan tsarin janye tallafin na mai.
Kodayake babban jami’in gudanarwa na kamfanin kula da albarkatun mai ta kasa (NNPCL), Mele Kyari, ya jaddada cewa babu sauran tallafin mai gaba daya a Nijeriya.
Ya shaida hakan ne a lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida a fadar shugaban kasa da ke Abuja bayan ganawa da suka yi da shugaban Bola Tinubu.
Idan za a tuna dai shugaban kungiyar (PENGASSAN), Festus Osifo, a ranar Jama’a ya yi ikirarin cewa gwamnati ta dawo da biyan tallafin mai, duk kuwa da cewa gwamnatin ta gabatar da tsarin janye tallafin mai tun a watan Mayu.
Sai dai, Kyari ya yi bayanin cewa sayar da mai da ake yi a wasu jihohi na farashi mai sauki ba shi ke nufin an dawo da biyan tallafin mai ba.
Ya ce gwamnati ta na dawo da cikakken kudinta daga kayayyakin da ake shigowa da su. Ya ce: “Babu tallafin. Muna dawo da cikakken farashinmu daga kayyakin da muke shigowa da su. Muna sayarwa a kasuwa, mun fahimci dalilin da ya sa ‘yan kasuwa ba su samun zarafin shigowa da kaya.
“Muna fatan za su yi hakan cikin gaggawa kuma wadannan suna ire-iren abubuwan da gwamnati ke yi, babu zancen tallafin mai.”
Dangane da dogon layukan mai da ake samu a wasu gidanen mai a sassan kasar nan, Kyari ya ce matsalar ta samu asali ne sakamakon rufewar wasu hanyoyi da suka hada depot-depot na arewacin kasa da kudancin kasar nan, hakan ya janyo tsaikon kai kayan zuwa wurare.
A wani matakin kuma shugaban Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL), Mallam Mele Kyari, ya yi hasashen cewa Nijeriya za ta fara fitar da man da aka tace a shekarar 2024.
Shugaban NNPC ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a taron kungiyar Makamashi da Gas ta Kasa ta Nijeriya (Pengassan) Energy and Labour Summit a Abuja, inda ya ce nan ba da jimawa ba kasar za ta kasance mai dogaro da kanta wajen samar da kayayyaki.
Kyari ya kuma ba da hujjar dalilin gwamnatin tarayya na cire tallafin man fetur, inda ya kara da cewa idan ba tare da yunkurin hakan ba, da NNPCL ta shiga fatara.
Ya ce Nijeriya na bukatar samun makamashi mai dorewa wanda aka dora kan albarkatun da ake da su da kuma maye gurbin wadanda aka rasa.
Kyari ya kuma ba da shawarar sauya tsarin sufuri zuwa wasu hanyoyin samar da makamashi, musamman sufurin jama’a, wanda a cewarsa, yana nufin Nijeriya dole ne ta yi duk mai yiwuwa don ganin an samu ci gaban da ake samu a kan motocin bas na Gas a fadin kasar.
Kan wadannan matsalolin LEADERSHIP Hausa ta tuntunbi wani masani mai sharhi kan tattalin arziri da harkokin rayuwa na yau da gobe, Alhaji Ahmad Gambo Aminu, ya ce, dole ne a ciyo bashi muddin ana son yin abubuwan da za su kyautata rayuwa a kasar nan, sai dai ya ce babbar matsalar ma ba ciyo bashin ba ne.
“Duk wanda ya yi cikakken nazarin halin da tattalin arzikin kasar nan ya samu kansa a gwamnatin da ta gabata, dole ne sabuwar gwamnati sai ta yi cikakken nazarin nemo hanyoyin kudaden domin tafiyar da wasu shirye-shirye.
“Matsalarmu a kasar nan ba ciyo bashin ba ne a ga amfaninsu a zahirance ne matsalar. Domin kowa ya sani an ciwo basuka a baya amma a zahirance wasu ne kawai suka azurta kawukansu.
“Ba za a samu nasarar kyautata rayuwar mutane a kasar nan ba har sai an yi yaki da rashawa da cin hanci na musamman. Muna fatan cewa Tinubu ba zai yi kuskuren da gwamnatin baya ta yi ba na barin wasu tsiraru su wawushe dukiyar al’umma.”
Dangane da janye tallafin mai kuwa, masanin ya ce kamatuwa ya yi gwamnati ta tabbatar da kashe rarar kudin da aka tara na tallafin da aka janye wajen raba wa ‘yan kasa muddin in da gaske ake yi. Sai ya ce, in fa hakan ba za ta samu ba, akwai bukatar a dawo da tallafin mai din har sai komai ya daidaita kafin a aiwatar da hakan.
Wasu al’ummar Nijeriya da muka zanta da su, balo-balo sun shaida irin ukuban da suke sha a gwamnatin nan sakamakon janye tallafin mai, “Abun bakin ciki da takaici yanzu fa ana maganar Tinubu ya maida kasar nan yadda ya sameta ne. Wannan alamun babban matsala ne a garemu,” Cewar Ishola Samuel, wani dan Nijeriya.
Samuel ya ci gaba da cewa, “Idan an ce tsiraru ne ke amfana da tallafin mai da ake bayarwa, yanzu kowa ya ji a jikinsa ya gane cewa tallafin na taimaka wa al’umma. Don haka ina shawartar gwamnati take nazari sosai kafin daukan kowani irin mataki.”
Shi ma Malam Muhammad Muslim, ya nuna irin wahalar rayuwa da ake sha, “Komai ya yi tsada, harkokin sufuri na kara rugujewa. Wallahi ana shan wahalar rayuwa fiye da tunanin ka. Mu dai muna fatan a dawo da tallafin mai kawai.”
Wasu ‘yan kasuwa kuma sun nuna damuwa kan yadda ake samun karancin ciniki sakamakon rashin kudi a hannun jama’a da tsadar kayan amfani, “Muma ba dadi muke ji ba. Mutum zai zo sayen kayanka ka na kukan ba riba ba kasuwa shi kuma ya na kukan ba kudi. Wannan yanayin sai dai mu hada da addu’ar neman mafita kawai,” cewar wani dan kasuwa, Alhaji Salisu Hababu na kasuwar Central da ke Bauchi.
Kazalika mun tattauna da wani direba, Ashuru Bello, inda ya ce yanzu duk kudin da suke samu a mai yake tafiya, “Malam abun da zan fada maka shi ne da yawan direbobi sun ajiye motocinsu, muddin aka ce maka motarka ba maka na kashin kanka ba ne to wahala kawai za ka sha domin abun da mota ke ajiyewa yanzu bai taka kara ya karya ba. Ka na sayen kudin zai kare.
“Abun damuwar ma shi ne babu fasinjojin wadanda suke yin tafiyar ma za ka samu na dole ne. Kuma su ma a cikin rokon ragi da korafi ake. Haka muke fama a wannan lokacin,” Ya shaida wa LEADERSHIP Hausa.
Source: LEADERSHIPHAUSA