A ranar 10 ga wata, shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya duba aikin gina tashar samar da wutar lantarki ta ruwa ta Kandaji wanda kamfanin CGGC na kasar Sin ke gudanarwa, inda ya nuna gamsuwa kan yadda aikin ke gudana.
Bazoum ya saurari rahotanni kan shirin gudanar da aikin gaba daya, yanayin rigakafin annoba, da ci gaban da aka samu kan gini.
Shugaban ya ce yana fatan dukkan bangarorin da suke gudanar da aikin, ciki har da kamfanin CGGC na kasar Sin, za su iya hadin kai sosai don kammala aikin cikin sauri, hakan zai ba da gudummawa ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma na Nijar.
Tashar samar da wutar lantarki ta Kandaji ita ce tashar samar da wutar lantarki ta ruwa ta farko da ake ginawa a Nijar.
An shigar da aikin cikin ayyukan “Shirin shekaru dari” na Nijar, kuma yana daya daga cikin muhimman ayyukan bisa shawarar “Ziri daya da hanya daya”.
Bayan kammala aikin, matsakaicin yawan wutar lantarki da za ta samar a ko wace shekara zai iya kaiwa kilowatts-awa miliyan 617.
Ba kawai za ta iya ba da tabbaci a fannin wutar lantarki don ciyar da tattalin arzikin Nijar gaba ba ne, har ila yau za ta inganta ci gaba da kyautata aikin jan ruwa ga gonakai, da samar da ruwan sha ga jama’a da kuma kyautata muhallin halittu.