Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Jama’atu Nasril Islam (JNI), Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya bukaci gudanar da addu’o’i na musamman da Allah Ya kawo dauki kan kalubalen rashin tsaro da ke addabar al’uma.
A wata sanarwa da babban sakataren JNI, Dakta Khalid Abubakar Aliyu, ya fitar ranar Alhamis a Kaduna, Amirul Muminin ya kuma bukaci alhazan Nijeriya da su yi wa Nijeriya da shugabanninta addu’a na musamman, yayin da suke tsaye a kan dutsen Arafat.
Sanarwar da ta fito daga fadar sarkin musulmi ta kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su nemi taimakon Allah domin samun kwanciyar hankali, tsaro da zaman lafiya da ci gaban Nijeriya a daidai lokacin da babban zaben shekarar 2023 ke gabatowa.
JNI, ta sake nanata bukatar yin addu’o’i sosai domin samun sauye-sauyen siyasa cikin lumana, da kuma kawo karshen kalubalen zamantakewa da tattalin arziki iri-iri a kasar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Idan aka yi la’akari da cewa al’amura guda biyu suna haduwa a ranar Juma’a, wato gobe akwai bukatar tunatar da musulmi da su yi azumin ranar 9 ga watan Zul-Hijja (Arafat), kamar yadda Annabi (SAW) ya koyar da shi.
Kasancewarta rana ta musamman ta Juma’a kuma ita ce mafificiyar ranar mako, a cikinta ake yin Sallar Juma’a da amsa addu’o’i a cikin sa’a ta musamman da Arafat.
Mafi kyawun ranar shekara a cikinta. Allah mai rahama yana gafartawa bayinsa kuma yana amsa dukkan addu’o’in ranar Arafat.
“Don haka Mai Martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, CFR, mni, ya bukaci al’umar Musulmin Nijeriya da su azumci ranar, kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya koyar kuma a yi addu’a neman Allah Madaukakin Sarki da ya shiga lamuranmu.
A wani labarin na daba al’ummar Musulmi fiye da miliyan guda na gudanar da aikin hajji a kasa mai tsarki, inda a yau juma’a su ke hawan Arafa wanda ke matsayin jigo a aikin hajji kuma wajibi ga dukkan musulmi.
A yammacin jiya alhamis ne tarin mahajjatan suka bar Makka zuwa birnin Mina inda suka yi kwanan Mustalifa gabanin hawan arafan a yau juma’a.
Rahotanni sun ce daga cikin adadin musulmin fiye da miliyan guda da ke gudanar da aikin hajjin, fiye da dubu 850 sun fito ne daga kasashen musulmi yayinda sauran suka fito daga cikin Saudiyya.
Duk da cewa adadin mahajjan nab ana sun dara yadda aka gani a shekaru biyu da suka gabata bayan bullar cutar corona, alkaluman mahajjatan bai kai na shekarar 2019 ba, lokacin da mutane miliyan 2 da rabi suka sauke farali.
Aikin Hajji na matsayin guda cikin rukunan addinin Islama da ke matsayin wajibi kan duk wanda ke da wadata, yayinda ake son kowanne musulmi ya gudanar da ita akalla sau 1 a rayuwarsa.
Dukkanin wadanda ke aikin hajjin a bana sai da suka nuna shaidar ko dai basa dauke da cutar corona ko kuma shaidar karbar rigakafin cutar kafin samun damar aiwatar da ibadar.