Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya biya wa sababbin dalibai 1,740 da suka samu gurbin karatu a jami’ar ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kano.
Gwamna Yusuf ya bayyana haka ne a ranar Asabar a lokacin kammala yayin bikin maraba da zuwa na dalibai masu karatun digiri na daya a makarantar.
A shekarar 2023 ne Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta amince da daga darajar Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kumbotso a Jihar Kano zuwa jami’ar ilimi.
Ya ce gwamnatin jihar ta himmatu sosai wajen tallafawa bukatun ilimi na dalibai ba tare da la’akari da siyasa ba.
Ya ce gwamnatin jihar ta kuma ware kashi 30 cikin 100 na kasafin kudinta na shekarar 2024 ga ilimi, wanda hakan yasa aka samu kari daga shekarun baya.
Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar, Dr. Ibrahim Kofarmata, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta yafe kashi 50 na kudaden makaranta na makarantun sakandire da manyan makarantun jihar domin samun saukin ilimi ga yara masu rauni.
Shugaban Jami’ar, Farfesa Yahaya Isa Bunkure, ya yabawa kokarin Gwamna Yusuf a kan harkar ilimi, ya kuma bayyana irin nasarorin da jami’ar ta samu, da suka hada da shirye-shiryen bunkasa ma’aikata, ayyukan bincike, da inganta ababen more rayuwa.
Bunkure ya ja kunnen daliban da su himmatu tare da yin azama da mayar da hankali a yayin da suke gudanar da karatunsu a jami’ar.
DUBA NAN: Kwale Kwale Yayi Sanadin Rasa Ran Dalibai Biyu A Kano
Bunkure, ya kuma samu lambar yabo ta ‘Fellowship’ daga Cibiyar Nazari ta (FNIP) saboda gudummawar da ya bayar a fannin da jajircewarsa wajen bincike da ilimi.