Gwamnatin jihar Kano ta rushe gine-ginen da aka yi a jikin filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata.
Freedom ta rawaito cewa, gwamnatin ta kuma rushe wasu Shaguna da ke jikin makarantar Sakandire ta Ƙofar Nassarawa ta fuskar titin IBB.
Sannan ta rushe gine-ginen da ke jikin makarantun Sakandire na Duka Wuya da ta Goron Dutse.
Ƙarin bayani zai zo muku a labaranmu na An Tashi Lafiya da ƙarfe 6 na safe idan Allah ya kaimu.
A wani labarin na daban ma’aikatar Noma da Raya Karkara ta Tarayya, a ranar Litinin, ta fadakar da jama’a game da yin taka tsantsan yayin da Arewacin Ghana da kan iyakar kasar Burkina Faso da Togo aka rahoto barkewar cutar Anthrax.
Anthrax cuta ce wacce da farko take shafar dabbobi amma takan iya yaduwa zuwa ga mutane ta hanyar hulda da dabbobin da suka kamu da cutar. Kamar shafar fata, cin nama ko shan nonon dabbar da ta kamu da cutar.
Sai dai, an bayyana cewa, Anthrax ba mai yaduwa ba ce a iska, ana iya kamuwa da ita ta hanyar mu’amala da wadanda suka kamu da kwayoyin cutar ne kawai.
Anthrax tana iya bayyana ta nau’i-nau’i daban-daban, ciki har da alamu masu kama da mura kamar tari, zazzabi, ciwon tsoka sannan kuma, idan ba a gano cutar da wuri an magance ta da wuri ba, zata iya haifar da ciwon huhu mai tsanani wacce za ta iya toshe numfashi ta kai ga mutuwa.
A cewar wata sanarwa da babban sakatare a ma’aikatar, Dr Ernest Umakhihe ya fitar; Jihohin Sokoto da Kebbi da Neja da Kwara da Oyo da Ogun da kuma Legas sun fi fuskantar hadari sabida kusancinsu da Burkina Faso da Togo da Ghana, don haka, ana bukatar a kara kaimi wurin yin allurar rigakafin dabbobi a wadannan jihohin dama daukacin jihohin tarayyar Nijeriya.