Red Cross; Miliyoyin Mutane Suna Fuskantar Yunwa A Nahiyar Afica.
Kungiyar agaji ta kasa da kasa “Red Cross” ta yi gargadin cewa, fadace-fadce da sauyin yanayi da kuma yadda farashin kayan abinci ke karuwa, za su jefa daya bisa hudu na mutanen Afirca cikin yunwa.
A jiya Talata ne kungiyar agajin ta duniya ta sanar da cewa; Da akwai mutane miliyan 346 da suke fama da matsananciyar yunwa,kuma abu ne mai yiyuwa adadin ya karu nan da wasu watanni.
A shekarar da ta gabata mutanen da yunwar ta addaba ba su wuce miliyan 286 ba a cikin nahiyar ta Afirca.
Wasu daga cikin kasashen na nahiyar Afirca da suke fama da yunuwa sun hada Somaliya, Habasha, Murtaniya da Burkina Faso.
Yakin kasar Ukiraniya ma ya kara sa matsalar abinci da makamashi sun ta’azzara ta hanyar hauhawar farashinsu da kuma kai su kasuwanni. Dama dai cutar korona ta taka tata rawar a wannan fagen na rubanya matsalar karancin abinci.
Shugaban bangaren da ke kula da ayyukan kungiyar ta ( Red Cross) na duniya, Dominik Stillhart, ya fada a birnin Nairobi na kasar Kenya cewa; RIkice-rikicin da ake yi a cikin kasashen da muke aiki sun dade da shafar harkar samar da abinci da kuma jefa mutane cikin abinda ya yi kama da fari.