Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Mr Peter Obi ya ce ba zai binciki gwamnatin Buhari da saura da suka shude ba.
Peter Obi ya sha nanata cewa ba zai yiwu mutum ya rufe shagonsa ya fara bin barayi ba, don haka zai mayar da hankali ne wurin dakile guraben bannatar da kudi.
Tsohon gwamnan na Jihar Anambra ya kara da cewa muddin shugaban kasa, gwamnoni, shugaban kananan hukumomi da saura tare da na kusa da su ba su sata, za a rage matsalar da kashi 70 cikin 100.
Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, LP, ya ce ba zai binciki gwamnatin da ta shude ba idan aka zabe shi ya zama shugaban kasa a 2023, rahoton The Cable.
Da ya ke magana a ranar Juma’a bayan gabatar da mataimakinsa Datti Baba-Ahmed, wanda ya kafa Jami’ar Baze.
Obi ya ce zai mayar da hankali ne wurin dakile wuraren da ake asarar kudi da kuma ciyar da kasa gaba.
“Batun bincikar gwamnatin baya, bari in fada muku; ku sha gani na ina cewa ba zai yiwu ka rufe shago kana bin barawo ba, wadanda jiya kawai suke kallo za su raba hango gobe.
Ubangiji bai bamu ido a baya ba, nawa na kallon gaba ne,” in ji shi. “Idan ka zo gwamnati yau kuma ka fara dakile inda kudade ke zuba, za ki fi samun nasara.
Ba zan bibiyi wani gwamnatin baya ba, ba za ta faru ba. Dole yan Najeriya su yi rayuwa bisa doka da oda.
“Amma zan iya fada maka yanzu, Idan kai a matsayin jagora, shugaban kananan hukuma, gwamna, shugaban kasa baka sata, iyalanka ba sa yi, kuma na kusa da kai basa yi, za ka rage abin da kashi 70 cikin 100.”
Na ce masa, abin da za mu yi ba mu biyu bane kawai,” in ji shi.
“Za mu janyo yan Najeriya cikin wannan babban tantin saboda muna son kawo karshen siyasan kabilanci da addini. Muna son maye gurbinsa da cancanta.”
Babban Sallah: Biyayya Ga Koyarwar Addini Zai Magance Mafi Yawancin Matsalolin Mu, Buhari.
A wani rahoton, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce idan yan Najeriya za su rika aiki da koyarwar addinai, da an warware mafi yawancin matsalolin da ke adabar al’umma, Nigerian Tribune ta rahoto.
A sakonsa na babban sallar ga musulmin kasar da sauran mutane a ranar Juma’a, Shugaba Buhari ya yi kira da al’umma su fifita kasa kan bukatun kansu kuma “su yi amfani da addini don zaburar da su son al’umma.”