Shugaban Hukumar Agajin Gaggarawa ta Kasa (NEMA), Mustapha Habib Ahmad ya bayyana cewa hukumarsa tare da hadin gwiwar hukumar hada kan Afrika (AUC) da kuma shirin Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) sun kuduri aniyar daukar matakai domin rage hatsari kwararowar hamada.
Ya ce kwararowar hamada na matukar barazana ga Nijeriya da kuma jawo asarar rayuka da dukiyoyin al’umma sakamakon dumamar yanayi da ke fuskantar kasashen Afrika da ma wasu kasashen duniya.
Mustapha ya bayyana hakan ne a lokacin taron kwana biyu na masu ruwa da tsaki a kan yaki da kwararowar hamada da hukumar NEMA ta shirya da ya samu halartar wakilai daga jihohin Nijeriya da ya gudana a Kano.
Ya ce dumamar yanayi da kwararowar hamada na haddasa bala’o’i a kasa kamar ambaliyar ruwa, wanda ke kawo yawan haduran jiragen ruwa da faduwar gine-gine da dai sauransu.
Ya jawo hankali masu ruwa da tsaki da mahalarta wannan taro kan su yi aiki sosai kan abun da aka tattauna a taron. Ya kuma ya yaba wa gwamnatin tarayya da kungiyoyin kasa da kasa.
A nasa jawabin, mataimakin Daraktan hukumar, Dakta Daniel Obot ya ce wannan aiki na yaki da kwararowar hamada sakamakon canjin yanayi ya kunshi kasashen Afrika bakwai da suka hada da Birkina Faso, Chadi, Mali, Martaniya, Nijar, Sanigal da kuma Nijeriya, wanda aka hada hannu wajen aiki domin kawar da kwararowar hamada.
Source: LEADERSHIPHAUSA