Bola Tinubu ya samu gudumuwa mai tsoka na yakin neman zaben shugaban kasa da ya ziyarci jihar Neja Motoci 100.
Sanata Sani Musa ya raba domin ganin Tinubu ya kai labari a karkashin jam’iyyar APC.
Sannan ‘Dan majalisar dattawan ya ba kyautar ofishi da za ayi amfani da shi wajen yin kamfe a 2023.
Motoci 100 Sanata Sani Musa ya bada a matsayin gudumuwarsa wajen yakin neman zaben Asiwaju Bola Tinubu a jam’iyyar APC a 2023.
The Nation ta kawo rahoto a ranar Laraba 14 ga watan Disamba 2022 cewa, ‘Dan majalisar ya taka rawar gani wajen ganin APC ta lashe zabe.
Sanatan Gabashin jihar Nejan ya bada kyautar motoci 100 da ofishi na musamman domin ya marawa Bola Tinubu baya ya zama shugaban kasa.
Da yake kaddamar da motocin da kuma ofishi a ranar Laraba, Sanata Sani Musa ya ce ya yi hakan ne saboda abin da zai je ya dawo ga mutanen Neja.
Abin da ya sa na raba motoci – Musa
“Na kaddamar da motocin nan da ofishin nan ne saboda mutanen Najeriya da kuma mutanen Neja a lokaci da kuma bayan yakin zaben shugaban kasa.”
Rahoton ya ce Sani Musa ya yi alkawarin za suyi bakin kokarinsu wajen karkato da ra’ayin mutane domin ganin sun zabi ‘dan takaran jam’iyyar APC.
Bola Tinubu a Neja
Haka zalika Sanatan ya ce za su dage wajen ganin an zabi duk wadanda APC ta tsaida.
Baya ga kyautar da ya ba kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu, Sanata Musa ya raba keke-napep ga wasu magoya bayan jam’iyyar APC da ke jihar.
‘Dan takaran APC PM News ta ce ‘yan majalisar wakilan tarayya da na dokokin jiha sun halarci bikin kaddamar da kayan, Musa yake cewa ya yi ‘dan abin da zai iya yi.
Wadanda suka yi wa Tinubu rakiya zuwa wajen taron kaddamar da gudumuwar sun hada da Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello da DG, Simon Lalong.
Sauran ‘yan tawagar ‘dan takarar shugaban kasar sun kunshi Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa da Gwamnan Kebbi, Atiku Abubakar Bagudu.
Malagi ya bada ofis
A rahoton da muka fitar a jiya, kun ji Bola Tinubu ya kaddamar da ofishin yakin neman takara da Mohammed Idris Malagi ya ba shi kyauta a Neja.
Shugaban gidan jaridar na Blueprint yana cikin jiga-jigan APC mai mulki, shi ne Darektan dabarun sadarwa na kwamitin yakin zaben Tinubu a 2023.