Kungiyar iyayen dalibai na Najeriya, NAPTAN, tana son bada gudunmawar ta domin ganin an kawo karshen yajin aikin ASUU.
NAPTAN na son yi wa gwamnatin tarayya tayin cewa kowanne iyayen dalibi/daliba za su rika biyan N10,000 duk zangon karatu a matsayin tallafi da za a bawa ASUU.
Iyayen daliban sun ce sune yajin aikin ya shi shafa don haka suka yi kira ga gwamnatin da ASUU su gaggauta warware matsalar da ke tsakanin su.
Kungiyar Iyayen Dalibai da Malamai na Najeriya, NAPTAN ta nemi ganawa da Gwamnatin Tarayya kan yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, wanda ya ki ci ya ki cinyewa.
Kungiyar tana son bada shawarar iyayen kowanne dalibi su rika biyan N10,000 duk zangon karatu don taimakawa gwamnati samun kudin shiga da za ta bawa jami’o’i, The Punch ta rahoto.
Kakakin NAPTAN, Dakta Ademola Ekundayo, ya bayyana hakan ne cikin hirar da The Punch ta yi da shi a ranar Talata.
Ekundayo, wanda ya koka kan cigaba da rufe jami’o’i a kasar ya ce iyaye ne suka fi kowa jin jiki sakamakon rikicin tsakanin gwamnatin tarayya da ASUU.
Ya ce: “Mun mika wasikar zuwa ofishin ministan ilimi, muna neman zaunawa da shi inda muke fatar gabatar musu matsayar mu.
“Muna son kowanne iyaye su rika biyan N10,000 ga jami’o’i duk zangon karatu.
Wannan zai zama gudunmawarmu baya ga wasu kudaden wurin ganin jami’o’i sun samu kudi.
“Ana iya kiransa tallafin iyaye ga jami’o’i. Mune muka fi shan wahala saboda yajin aikin.
Muna rokon ASUU da gwamnatin tarayya su warware matsalolinsu nan take.”
A wani rahoton, gwamnan Jihar Ebonyi kuma shugaban kungiyar gwamnonin Kudu maso Gabas, David Umahi ya ce ilimin Jami’a fa ba na kowa da kowa bane, rahoton The Punch.
Umahi ya jadada cewa ba adalci bane a yi tsammanin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ciyo bashin fiye da Naira tiriliyan 1 don biyan bukatun ASUU.
Gwamnan ya yi wannan jawabin ne kan yajin aikin da malaman jami’o’i ke yi, a lokacin da ya karbi bakuncin tawaga daga asusun yan sandan Najeriya karkashin jagorancin Dr Ben Akabueze, a Abakaliki a ranar Laraba.
Source: LEGITHAUSA