Najeriya; Karin Farashin Man Fetur Da Gwamnati Ta Yi Na Ci Gaba Da Shan Martani.
Bisa sanarwar da masu hada-hadar man fetur a Najeriya suka fitar, bisa umarnin gwamnatin tarayya an kara farashin kudin man fetur a fadin kasar.
Bisa rahoton gidan rediyon Faransa, karin farashin ya fara aiki daga jiya Talata, inda har aka sayar da lita guda akan Naira 179 kudu maso yammaci da kudu maso kudanci da kuma kudu maso gabashin Najeriya.
Haka nan kuma a arewa maso yammacin kasar kuwa, farashin ya kai Naira 184 , sannan ana sayar da lita guda akan Naira 189 a yankin arewa maso gabashin kasar, abin da ke nufin an kara Naira 24 rigis.
A yankin tsakiyar arewacin kasar kuwa farashin zai kasance akan Naira 179 , yayin da a birnin Lagos za a ci gaba da sayar da farashin akan Naira 169, sannan kuma a Abuja farashin zai kasance akan Naira 174 a kan kowace lta guda.
Sai dai jama’a da dama a kasar suna nuna damuwa dad a matakin, wanda suke kallonsa a matsayin abin da zai kara yawan wahalhalun da suke fama da su, duk da cewa a aikace dama ana sayen man fetur a gidajen man ‘yan kasuwa a kan farashin da ya haura hakan tun daga farko-farkon wannan shekara har zuwa yanzu.