Najeriya; Jami’an Gwamnati Suna Iya Shiga Harkokin Siyasa Ba tare Da Sun Bar Ayyukansu Ba.
‘Yan sayasa kuma jami’an gwamnati a tarayyar Najeriya a halin yanzu basa bukatar barin mukamansu na gwamnati don shiga harkokin siyasa. Jaridar Leadership ta Najeriya ta nakalto mai sharia Evelyn Anyadike na babban kotun tarayyar a garin Ummuahia na jihar Abia yana yanke hukuncin hakan.
Mai shari’an ya bayyana cewa dokar zabe wacce shugaba buhari ya sanyawa hannu a cikin yan makonnin da suka gabata, wato dokar zabe mail aba 84(12) bata bisa ka’ida, don ta sabawa kundin tsarin mulkin kasar wanda ya halattawa yan siyasa rika mukamansu a lokacinda suke harkokin siyasa.
Wani bangare na dokar zaben ta bayyana cewa dole ne jami’an gwamnati ‘yan siyasa su ajiye mukamansu a lokacinda suke shiga harkokin siyasa.
READ MORE : A Yau Ce Kasar Iran Take Tunawa Da Kafa Dokar Maida Kamfanin Man Fetur Na Kasar Ya Zama Na Kasa.
Har’ila yau ministan sharia na kasar Abubakar Malami ya bayyana cewa gwamnati zata yada wannan hukunci a kafafen yada labaranta don yan siyasa su yi amfani da shi.
Labarin ya kara da cewa kafin haka shugaba Buhari ya bukaci majalisun dokokin kasar su shafe wannan bangare na dokar zaben a lokacinda yake sanya mata hannu, don ta sabawa kundin tsarin mulkin kasar.