Najeriya; IPMAN Ta Ce Babu Albashi Ga Ma’aikatanta Da Ba Su Da Katin Zabe.
Ƙungiyar Dillalan Man fetur ta Ƙasa, IPMAN, ta yi barazanar hana ma’aikatanta albashi har sai sun yi katin zaɓe na dindindin, PVC.
Wannan ya biyo bayan umarnin da Shugaban IPMAN na ƙasa, Chinedu Okoronkwo, ya bayar, inda ya bukaci ma’aikatan ƙungiyar a duk fadin ƙasar da su je su yi katin zaɓe kafin cikar wa’adin da INEC ta bayar na rufe yin rijistar a ranar 30 ga watan Yuni.
Sharaɗin ƙin biyan albashin na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban ƙungiyar reshen Jihar Kano, Bashir-Danmallam ya fitar a yau Juma’a a Kano.
Danmallam ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne a wani taro da Okoronkwo, wanda ya umarce shi da ya fitar da sanarwar.
“Kungiyar ta gano cewa ya zama dole ta ɗauki matakin don tabbatar da cewa duk mambobinta da suka cancanta sun sami PVC don ba su damar nuna hakkin su na ƴan ƙasa a babban zaɓen 2023.
“Mu ba mu ce ƴan ƙungiyar mu su zaɓi wani dan takara ko jam’iyyar siyasa ba, amma damuwarmu ita ce mambobinmu su samu katin zabe na PVC, domin idan ba tare da ita ba, ba za a iya zabe ba.
“mu na kira ga mambobinmu da su je su zaɓi wanda su ke gani ya fi musu a cikin ƴan takarar shugabancin Kasar nan a zaɓe mai zuwa a kowacce jam’iyar,” in ji shi.