A cewar Hukumar Aikin Hajjin ta Nijeriya (NAHCON), duk da Shugaban Hukumar Aikin Hajjin, Malam Jalal Ahmad Arabi, ya so kudin Hajjin Bana ka da ya haura abun da maniyyatan suka ajiye na naira miliyan hudu da rabi, farashin dala ya hana hakan ya kasance.
Shugaba Jalal Ahmad Arabi, ya yi iya yinsa don kamfanoni masu yi wa Alhazai hidimar tafiyar su karyar da farashinsu, wanda hakan yasa aka samu saukin farashin kujerar ta bana don da kudin kujerar sai ya haura sama da miliyan shidda.
Maniyyata daga Kudancin Nijeriya za su biya: Naira miliyan hudu da dubu dari takwas da casa’in da tara wato (N4,899,000), sai Maniyyatan da suka fito daga yankin Arewa kuwa za su bayar da Naira miliyan hudu da dubu dari shidda da casa’in da tara wato (N4,699,000), sai kuma Maniyyata daga Jihohin Borno da Adamawa inda za su biya naira miliyan hudu da dubu dari shida da saba’in da tara watau (N4,679,000) don zuwa sauke Faralin shekarar dubu biyu da ashirin da hudu (2024).
Shugaban NAHCON ya ce yana la’akari ne da wa’adin da kasar Saudiyya ta bayar na 25 ga watan da muke ciki na Febrairun 2024 a matsayin ranar da za a rufe biyan kudaden.
Saboda haka ya zama dole maniyyata su kammala cikasa kudinsu kafin ko kuma kada ya gota ranar Litinin sha biyu ga watannan na fabrairu don NAHCON ta iya aike wa kudaden zuwa Saudiyya kafin cikar wa’adin da ta gindaya.
NAHCON ta ce, tana fatan ganin an samu cikakkiyar nasarar gudanar da Hajjin Bana duk da kalubalen da ake da su da kuma jinjinawa Musulman Nijeriya, saboda hadin kan da suka bayar cikin wannan yanayi na rashin-tabbas da ake ciki.
Source: LEADERSHIPHAUSA