Kamar yadda suka saba almajiran jagoran harkar musulunci a Najeriya watau Sheikh Ibrahim Yqoob Alzakzaky sun gabatar da jerin gwano wanda ak fi sani da muzahara a babban birnin tarayyar Abuja, muharar dai na zaman kira ga gwamnatin Muhammadu Buhari da ta gaggauta sakin takardun tafiyar Jagoran da na mai dakin sa malama zinatu ibrahim domin su tsallaka kasashen ketare domin ganin kwararrun likitoci.
Kamar yadda membobin harka islamiyyan suka bayyanawa wakilin yayin da suke tsaka da gwabatar da muzaharar sun bayyana cewa fitowar ta yau domin kira ne a saki fasfunan jagoran kamar yadda doka ta bukata gami da Allah wadai da kashe kashen da ake ta faman yi a arewacin Najeriya.
Muzaharar wacce aka gudanar da ita a ranar 8 ga watan yuli ta dauki hankalin mutane da dama kuma ta isar da sakonni mabambanta ga gwamnati dama sauran al’ummar gari.
Idana ba’a mance ba dai Malam zakzaky wanda ya share kusan shekaru takwas a hannu jam’ian tsaron Najeriya bayana an tuhume shi da zargin hadin baki wajen aikata kisan kai tun lokacin da sojoji suka kai hari gidan sa dake gyallesu a zariya.
Babbar kotu a kaduna ta saki shehin malamin inda ta wanek shi kuma ta tabbatar da cewa bai aikata laifin komi ba.
Amma sai dai tun wancan lokaci a ka jiyo almajiran malamin suna kokwa inda suka bayyana cewa ‘Ba cinya ba kafar baya’ domin shehin malamin yana fama da matsananciyar rashin lafiya shi da mai dakin sa kuma suna bukatar fita kasashen ketare domin kwararrun su duba lafiyar su a,,a gwamnatin Najeriya karkashin shugaba buhari ta hana shi fasfunan su.
Muzaharar almajiran malam zakzaky dai ba bakuwa bace a birnin Abuja kamar yadda kundin tsarin mulki ya bama kowanne dan kasa ya fito ya bayyan ra’ayin sa suma mambobin harka islamiyya ba’a barsu a baya ba wajen amfani da wannan dama.