Gwamnatin Tarayya ta ce za ta samar da manhajar tsarin rancen kudin dalibai.
Hakan ya fito ne a cewar Babban Sakataren Hukumar Kula da Rancen dalibai, Akintunde Sawyer, wanda ya yi magana a ranar Litinin bayan da hukumar ta gana da Shugaban Kasa Bola Tinubu a Abuja.
Sawyer, ya ce an dauki wannan matakin ne domin tabbatar da an kawar da duk wani katsa-landan na mutane cikin harkokin tafiyar da tsarin wanda ake da shirin farawa a wannan shekara.
Wannan ci gaban na zuwa ne watanni bayan Shugaba Tinubu, ya ce shirin zai fara ne a watan Janairun 2024.
“A watan Janairu 2024, sabon tsarin lamunin dalibai dole ne ya fara.
A nan gaba kadan muna masu tabbatarwa da yakinin cewa ‘ya’yanmu da dalibanmu albishir na babu sauran yajin aiki,” in ji Tinubu.
Shugaba Tinubu a bikin ranar 12 ga watan Yuni, ranar dimokuradiyya, ya rattaba hannu kan kudirin ba da lamuni na dalibai domin cika alkawarin da ya dauka a lokacin yakin neman zabensa.
Kudirin dokar wanda Shugaban Majalisar Wakilai ta tara, Femi Gbajabiamila, wanda yanzu shi ne Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, ya dauki nauyinsa.
Ya samar da sauki ga ‘yan Nijeriya masu karamin karfi wajen samun guraben manyan makarantu ta hanyar lamuni mara kudin ruwa daga asusun bayar da lamuni na ilimi.
Kudaden shirin zai kasance a cikin ma’aikatar ilimi kuma daliban da ba su da karfi na manyan makarantu za su samu damar shiga.
Source LEADERSHIPHAUSA