Mabiya Malam Ibrahim Zakzaky wadanda aka fi sani da ‘yan shi’a sunyi taron tunawa da shekara takwasa da kisan kiyashin ranar kudus da akayi a lokacin mulkin Jonathan Goodluck wanda aka kashe akalla mutane 34 cikii harda ‘ya’yan malam zakzaky guda 3.
Mabiya Malam Zakzaky sun kuma sha alwashin cigaba gwagwarmaya har sai sunyi nasara a kan zalunci kuma sun tabbatar da juyin juya hali a Najeriya domin daidaito gami da samar da adalchi a kasa.
Sun kuma tabbatar da cewa zasu cigaba da gwagwarmaya har sai sun tabbata da an hukunta wadanda ke da hannu a kisan mambobin su a ranar qudus din shrkara takwas da ta gabata.
Da yake magana da manema labarai a makabartar da aka binne wadanda aka aka kashe a ranar qudus din daya daga cikin mabiya Malam Zakzaky, Abdulhamid bello ya bayyana cewa, yanzu taron tunawa da shahidan ranar Qudus na zariya ya zama taron da ake gudanarwa duk shekara.A
A ranar 24 ga july shekarar 2014 sojoji suka dira kan mambobin harkar ta musulunci karkashin jagorancin Malam Zakzaky inda suka kashe mutane 31 da kuma ‘ya’yan malamin 3.
Ba tare da wani dalili ba sojoji suka bude wuta kan masu muzaharar lumana domin nuna goyon baya ga raunanan falasdinawa, inji Bello
Harkar musulunci a Najeriya karkashin jagorancin Shehin malami Ibrahim zakzaky dai ta haura shekaru arba’in tana gudanar da ayyukan ta ciki da wajen Najeriya ba tare da aiwatar wasu ayyukan tada zaune tsaye ba kuma ckin buyayya ga dokokin Najeriya.
A disambar shekarar 2015 ne kuma sojoji suka kuma kai hari kan mabiya malam zakzaky a unguwar gyallesu inda suka kashe fiye dubu kuma suka jikkata da dama ciki har da jagoran harkar Malam Zakzaky tare da mai dakin sa Malama zinat.
Babu sanannen dalilin wannan hari amma majiyoyi mabambanta suna tabbatar da cewa an kai harin ne saboda cika umarnin masarautar saudiyya na dakile shi’anci a yammacin afirka.