Gwamnatin jihar Kano ta baiwa ma’aikatan jihar tabbacin fara biyan albashin watan Yuni a yau Litinin 26 ga watan Yuni, 2023.
Babban Akanta Janar na jihar, Alh. Abdulkadir Adussalam, ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a Kano ranar Lahadi.
A cewarsa dukkan ma’aikatan gwamnati za su rika karbar albashin su ne a ranar 25 ga kowane wata kamar yadda gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya umarta.
Abdulkadir ya ce sabbin ma’aikatan da aka dauka ba za su karbi albashin wannan wata ba saboda tantancewar da gwamnatin jihar za ta yi kan sahihancin tsarin daukar ma’aikata kafin su fara karbar albashi duk wata.
Akantan ya kuma bayar da tabbacin cewa duk wani kudi da ake cirewa ma’aikata a albashin su ba bisa ka’ida ba, gwamnati mai ci tana bayar da tabbacin kowa zai samu cikakken albashinsa har da ‘Yan fansho.
A wani labarin na daban gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya bayyana kudurin sake gina katafaren shatale-talen gidan gwamnatin jihar da aka rusa a kwanakin baya a wani wuri mafi da cewa – gadar Naibawa da ke wajen birnin jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yayin da yake gana wa da mai zanen shatale-talen ‘Golden Jubilee’ Kaltume Gana a sabon wurin da za a sake gina shatale-talen.
Gwamnan Yusuf ya sake nanata kudirin gwamnatisa na samar da ababen more rayuwa ga al’ummar jihar.
Ya ce wurin ya dace da zanen kuma ba zai haifar da wani kalubalen tsaro ba bayan gudanar da cikakken bincike, ya kuma sake tabbatar wa ‘yan jihar cigaba da samar da ayyukan more rayuwa masu inganci.
Mai zanen, Kaltume Gana ta gode wa gwamnan bisa yaba wa da aikinta na kwarewa da fasaha ta musamman.