Babban lauyan kuma daya daga cikin lauyoyin da suka jagoranci shari’ar jagoran mabiya darikar shi’a na najeriya sheikh ibrahim zakzaky, ya tabbatar da cewa batun da ake yadawa na daukaka karar gwamnatin jihar kaduna biyo bayan kayen da ta sha a satin daya gabata cewa hakan shirme ne kuma wani abu ne da za’a iya kamantawa da borin kunya ko kuma naje tabarmar kunya da hauka.
Barista Isahaq Adam ya bayyana cewa a matsayin su na lauyoyin malam zakzaky zuwa yanzu basu samu wata takarda da take nuna an shigar da kara a kowacce irin kotu ba.
Lauyan ya bukaci magoya bayan malam zakzaky da su kauda kai daga batun daukaka karar da gwamnatin ta kaduna take ta faman yada farfaganda domin ko[da ace ma sun daukaka zasu kuma shan kaye domin basu da hujja kuma duk wata tuhuma a kan wanda suke karewa ba ta da makama balle tushe.
Lauyan ya tabbatar da cewa batun daukaka kara babbar kotun gwamnatin tarayya dake kaduna kuma bashi da sahihanci domin a halin yanzu alkalan wannan kotu suna hutu ne kuma ba zasu dawo ba sai bayan akalla watanni biyu masu zuwa saboda haka babu wannan batun.
Lauyan ya tabbatar da cewa basa tsoron duk wani mataki na shari’a da gwamnatin kadunan zata kuma dauka domin sun tabbatar gwamanatin kaduna ba zata taba nasara a kowacce irin kotu ba domin basu da hujja bisa abinda suke ikirari.
Lauyan ya kwantar da hankalin al’umma inda yace koda gwamnatin ta kaduna ta kuma shigar da wata kara, to doka bata bada damara sake kama malam zakzaky ba kuma ma ba bukatar ya dinga halartar kotun illah iyaka lauyoyin sa ne zasu dinga halartar kotun, yayin da shi kuma zai cigaba da harkokin sa kamar yadda ya saba ciki har da tafiye tafiyen kasashen krtare duk doka bata hana shi ba.
Ana dai sa ran malam zakzaky zai fita kasashen ketare domin neman magani kamar yadda kowa ya sani yana fama da rashin lafiya shi da mai dakin sa.