Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta alanta cewa ta zabi Barista Ladipo Johnson a matsayin abokin tafiyar dan takarar shugaban kasar jam’iyyar, Rabiu Musa Kwankwaso.
Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit Johnson wanda dan asalin jihar Legas ya yi takarar gwamna jihar.
NNPP tayi wannan sanarwa ne a shafinta na Tuwita, @nnpphqabuja1, kuma Kakakin jam’iyyar, Major Agbor, ya tabbatar da hakan, rahoton Leadership.
10 Jawabin yace: “Barr Ladipo Johnson ne dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasar jam’iyyarmu mai girma.”
A wani labarin na daban kuma yau ake kada kuri’ar zaben gwamnan jihar Ekiti a Najeriya, inda aka tsaurara matakan tsaro.
Akalla rumfunan zabe dubu 2 da 445 ne ake sa ran an bude domin baiwa jama’a damar jefa kuri’un zaben sabon gwamnan a jihar ta Ekiti mai kananan hukumomi 16.
Ana sa ran fafatawa tafi zafi tsakanin da takarar jam’iyyar APC mai mulki, Abiodun Oyebanji da kuma tsohon gwamnan jihar, Segun Oni, dan takarar jam’iyyar SDP, sai kuma dan takarar PDP, Bisi Kolawole.
A halin da ake ciki, hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta ce za ta fara aiki da sabon tsarin wallafa sakamakon zabe kai tsaye ta na’ura mai kwakwalwa a zaben gwamnan na Ekiti, karon farko da za a aiwatar da sabon tsarin zaben, tun bayan sabuwar dokar gyaran zaben da shugaba Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu.
Gabanin zaben na yau alkaluman hukumar ta INEC sun nuna cewar mutane fiye da dubu 700 ne suka cancanci kada kuri’a a zaben Gwamnan.