Rahotanni daga Mali sun ce, masu ba da shawara kan harkokin soji na kasar Rasha sun isa Mali a cikin ‘yan makwannin nan, a daidai lokacin da ake samun takun saka tsakanin kasar da kasashen yammacin Turai dangane da zargin da suke yi mata na shirin daukar sojojin haya daga kamfanin Wagner na Rashan.
Wani jami’in, da shima ya nemi a sakaya nasa sunan, ya tabbatar da cewa ttuni masu ba da shawara na Rasha suka kasance a yankuna da dama na kasar ta Mali.
A karshen watan Disamba, kasashe 15 na yammacin duniya suka yi Allah wadai da zargin tura sojojin haya na kamfanin Wagner zuwa Mali, tare da zargin gwamnatin Rasha da hannu cikin shirin.
Sai dai gwamnatin Mali ta musanta zargin, tare da kalubalantar kasashen da su bada hujjar tabbatar da zargin nasu, inda kuma ta kara da cewar, kwararrun masu horas da sojoji na kasar Rasha ne suka isa kasar domin karfafa aikin jami’an tsaronta.
A wani labarinnna daban Gwamnatin Rasha ta sha alwashin ci gaba da hadin gwiwar soji da kasar Mali da kuma kare martabar yankin Sahel, yayin da ta musanta alaka da wasu ‘yan kwangilar soja da ake danganta su da kasarta.
Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce, sun fahimci bukatar tallafa wa Mali wajen yaki da ta’addanci a wata tattaunawa da ya yi da takwaransa na Mali Abdoulaye Diop a birnin Moscow.
Lavrov ya ce, suna samar wa kasar kayan aiki da makamai da harsasai, kuma za su yi duk abin da ya dace don dakile barazanar da kasar Mali ke fuskanta.
Ya ce, kamata ya yi a mika tambayoyi kan rawar da sojojin haya na Rasha ke takawa a kasar zuwa ga mahukuntan kasar Mali, kuma matakan soji da ‘yan kasar Rasha masu zaman kansu suka kafa ba aikin Rasha ba ne.
Ya kara da cewa idan aka kulla wadancan kwangilolin da halastattun gwamnatocin kasashe masu cin gashin kansu, ban fahimci abin da ake iya gani mara kyau ba game da hakan.
Rahotanni sun ce, yarjejeniyar na zuwa ne a daidai lokacin da Faransa ke shirin rufe sansanoni a Mali inda sojojinta ke yaki da masu kaifin kishin Islama tun shekara ta 2013, sai dai abin da bayanai ke cewa a yanzu shi ne, rikicin sojan da ya kunno kai tsakanin wadannan kasashe na da alaka da rikice-rikice a Ukraine, Afirka da kuma Gabas ta Tsakiya.