Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tabbatar da cewa su na kan tattaunawa da ‘yan jam’iyyar LP.
Akwai yiwuwar ‘Dan takarar shugaban kasan na jamiyyar NNPP ya hade da su Peter Obi a 2023 Hakan ta sa duk Jam’iyyun ba su fitar da asalin ‘yan takararsu na mataimakin shugaban kasa ba.
‘Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar hamayya ta NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya zanta da manema labarai a kan shirin 2023.
A wasu hira da aka yi da shi a gidajen rediyon BBC Hausa da VOA Hausa, Rabiu Musa Kwankwaso ya shaida cewa su na ta tattaunawa da bangaren Peter Obi.
Kamar yadda mu ka samu labari a safiyar Asabar, 18 ga watan Yuni 2022, Sanata Rabiu Kwankwaso yana kokarin ganin yadda za a bullowa 2023.
Wani Hadimin tsohon gwamnan na jihar Kano, Saifullahi Muhammad Hassan ya tabbatar da wannan magana a shafinsa na Facebook a daren na Asabar.
A gajeren jawabin da ya fitar, Saifullahi Muhammad Hassan bai yi wani karin-haske ba, sai dai kurum ya tabbatar da rade-radin da ke ta faman yawo a gari.
Abokin takara na wucin-gadi A tattaunawarsa da VOA Hausa, Kwankwaso ya ce tuni jam’iyyar NNPP ta bada sunan abokin takararsa a zaben 2023, amma wanda aka zaba na wucin-gadi ne.
Ana sa ran idan tattaunawar da NNPP da take yi da sauran jam’iyyu ta kammala, jam’iyyar za ta bada sunayen wadanda za su yi mata takara a zaben na badi.
Da ya zanta da BBC, Kwankwaso yace ba a gama magana ba, kuma bai fito karara ya fadi wanda zai yi takarar shugaban kasa da wanda zai yi na mataimaki ba.
Sai dai tsohon Gwamnan ya nuna za a duba matsayi wajen zaben wanda ya fi dacewa da takara.
Rataya aka ba ni – Doyin Okupe A daren nan aka ji Doyin Okupe wanda shi ne wanda jam’iyyar LP ta bada sunansa a matsayin abokin takarar Peter Obi, yana bayanin halin da ake ciki.
Dr. Doyin Okupe ya fadakar da magoya bayansu cewa an mikawa INEC sunansa ne kurum saboda gudun wa’adin da aka ba jam’iyyu ya wuce a ranar Juma’a.
Darekta Janar din na yakin neman zaben Obi ya ce wannan mataki da aka dauka zai bada dama a karkare maganar taron dangin da kananan jam’iyyu ke yi. Kamar yadda Kwankwaso ya fada, Okupe ya ce idan abubuwa sun tabbata, LP za ta fitar da ‘yan takara.
Atiku yana ruwa a PDP – Yaran Wike Biyo bayan ba Ifeanyi Okowa takarar mataimakin shugaban kasa a PDP, an ji labari jiga-jigan jam’iyya sun ce Atiku Abubakar ya saurari sakamakon zabe.