Jigo a jam’iyyar APC mai suna Kwamared Sabo Muhammad ya bayyana cewa a bisa dogaro da yanayin siyasar Jihar Bauchi da kuma abubuwan da suke faruwa a siyasance, al’ummar Jihar Bauchi su na jiran ranar zabe ne kawai su zabi dan takarar APC, Ambasada Sadik Baba Abubakar a matsayin gwamnansu.
Kwamared Sabo ya bayyana hakan ne a ganawarsa da wakilinmu a Bauchi, yana mai cewa alkawuran da gwamna Bala Muhammad ya yi wa jama’a a lokacin zaben 2019 da dama bai cika musu ba, don haka suke da fatan cewa APC za ta dawo mulki a jihar domin share wa al’umma hawaye.
Ya ce, daga cikin alkawuran da Gwamna Bala Muhammad ya yi a lokacin zaben 2019 sun hada batun tsaftace hidimar albashi, biyan albashi a kan lokaci, biyan kudin giratuti, biyan kudin hutu ga ma’aikata, gami da musu karin girma tare kuma da inganta kima da mutuncin sarakuna, ya ce wasu alkawuran da dama gwamnan bai cika ba.
“Bisa dogaro da irin wadannan muke da karfin gwiwa a kan Ambasada Air Mashal Sadik Baba Abubakar, don ya kasance dan Jihar Bauchi ne mai kishi, kuma ya yi aiki a bangaren soja har ya kai kololuwa mukami, sannan ya bauta wa kasa tsakani da Allah har ya samu yabo da jinjina daban-daban daga gwamnatin tarayya, musamman daga wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda zuwa yanzu suka kasance su ne hafsoshin Nijeriya da suka fi kowanne dadewa a kan karagar mulki, wanda su na kammalawa bisa irin gudunmawar da suka bayar sai ya saka musu da kujeran Ambasada.”
Ya kuma ce, duk mukamin da Sadik ya rike bai taba mancewa da jiha ba, ya samar wa mutane ayyukan yi, ya kawo makarantar soja da asibiti da filin jirgi na soja a Jihar Bauchi.
Source:Leadership