Wasu Kwamandojin kungiyar Boko Haram sun yi karin haske kan irin rayuwar da shugabansu marigayi Abubakar Shekau ya yi.
Kwamandojin da suka mika wuya ga rundunar sojojin Najeriya sun bayyana cewa Shekau ya mutu ya bar ‘kwarkwara 83.
A cewar kwamandojin, shugabansu Shekau na nan a wutan jahannama saboda ya aikata abun da ya saba da koyarwarsa ta hanyar kashe kansa.
Rahotanni sun kawo cewa tsohon shugaban kungiyar ta’addanci na Boko Haram, Abubakar Shekau, ya mutu ya bar ‘kwarkwara 83.
Wasu mayakan kungiyar ta’addancin da suka mika wuya ga sojojin Najeriya ne suka bayyana hakan.
Daily Trust ta rahoto cewa Shekau ya mutu ne a filin daaga lokacin da suke arangama da abokan hamayya a dajin Sambisa da ke jihar Borno a watan Mayun 2021.
Da yake jawabi a Maiduguri a ranar Asabar, mai ba gwamnan jihar Borno shawara ta musamman kan tsaro, Birgediya Janar Abdullahi Ishaq mai ritaya, ya ce ya samu bayanin ‘kwarkwarar ne daga wasu hadiman marigayi Shekau.
Ya ce wadannan hadimai sun mika wuya ga rundunar sojojin Najeriya sannan suka rungumi zaman lafiya.
Jaridar The Cable ta rahoto yana cewa:
“Mun fara wannan watanni 16 da suka gabata, ya fara ne jim kadan bayan mutuwar Abubakar Shekau sannan gwamnatin jihar bata so ISWAP su ci gaba da amfani da mayakan Shekau; mun san hakan zai zamo mai hatsari.
“Saboda haka, mayakan farko da muka tarba a Bama sun fada mani cewa Shekau na da ‘kwarkwara 83, ku ji fa ya bar ‘kwarkwara 83.”
Shekau na jahannama
Da yake ci gaba da jawabi game da tsohon shugaban na Boko Haram, Ishaq ya ce tubabbun mayakan sun bayyana cewa Shekau na nan a Jahannama.
“Sun ce yanzu yana wutar jahannama saboda ya kashe kansa ne a yayin arangama da daya bangaren.
A kullun yana fada masu su fita su yi yaki, idan ya mutu a cikin haka yan mata da dama na nan suna jiransu.”
Har ila yau ya ce mayaka da dama sun yi danasanin abubuwan da suka aikata, yana cewa Shekau ya batar da su.
Ya kara da cewar mayaka da dama basu san yadda ake alwala ba.
Malam Rugurugu: Kwamandan Boko Haram ya fadi dalilinsa na mika wuya
A wani labarin, kwamandan Boko Haram da ya tuba, Malam Rugugu ya bayyana cewa ya ajiye makaman yakinsa bayan ya yiwa kansa wa’azin ta nutsu.
Tsohon dan ta’addan ya ce ya gano cewa abun da yake aikatawa ba daidai bane don haka ya lallashi mayakansa suka fito daga jeji.