Kungiyoyin kwadago da suka hada da kungiyar ma’aikata (NLC) da ta ‘yan kasuwa (TUC) sun dakatar da yajin aikin da suka shirya tsunduma a ranar Laraba, sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.
Dakatar da yajin aikin ya biyo bayan wata ganawa da kungiyoyin suka yi da wakilan gwamnatin tarayya.
Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ne ya jagoranci tawagar gwamnati inda ya bayyana wa kungiyoyin kudurin gwamnati akan shirinta na magance koken kungiyoyin.
A cewar kakakin majalisar, gwamnatin tarayya da TUC da kuma NLC za su kafa wani kwamitin hadin guiwa da zai duba shawarar duk wani bukatar karin albashi da kuma tsari da lokacin aiwatar da tsarin.
Ya ce, gwamnatin tarayya da TUC da kuma NLC za su sake duba tsarin musayar kudi da bankin duniya ke bayarwa tare da tabbatar da cewa an sanya masu karamin karfi a cikin shirin.
A wani labarin na daban Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad ya fara wa’adin mulkinsa na biyu da daukar sabbin ma’aikata 1,684 a bangarori daban-daban na aikin gwamnati.
Hakan na kunshe ne cikin manufar shawo kan karancin ma’aikatan da ake fuskanta a wasu ma’aikatu, fannoni da rassan gwamnati.
Da yake zantawa da ‘yan jarida kan wannan lamarin, shugaban ma’aikatan jihar Bauchi, Alhaji Yahuza Adamu Haruna, ya shaida cewar, daga cikin ma’aikatan, sama da mutum dubu daya an dauke su ne a bangaren koyar da ilimi domin shawo kan matsalar da ake fuskanta a harkar ilimi a jihar.
Ya ce, malaman da aka dauka sun kunshi har da masu kuyar da muhimman darussa da suka hada da na turanci, lissafi, biology, Biology, Chemistry, Physics da kuma na ICT. Dukka a bangaren ilimin, ya kuma sanar da cewa, gwamnan ya kuma amince da daukan wasu karin malamai guda 154 da za su yi aiki a kwalejin koyar da ilimi ta Aminu Saleh da ke Azare.
Idan za ku tuna dai, a jawabinsa na shan rantsuwar kama aiki a matsayin gwamnan jihar Bauchi karo na biyu, Bala Muhammad ya shaida cewar, jihar ta cire takunkumin daukan ma’aikata domin bai wa matasan da suka dace cikakken damar shigowa a dama da su wajen tafiyar da aikin gwamnati, kan hakan ne ya nuna cewa kwanan nan za a fara daukan sabbin ma’aikata.
Yahuza ya ce, gwamnati mai ci a jihar ta Bala Muhammad ta himmatu wajen tabbatar da aiki mai inganci domin kyautata rayuwar al’umma da cigaban Jihar Bauchi.
Ya ce, “Sannu a hankali gwamna Bala Muhammad ya amince da fara daukan ma’aikata, inda ya amince da daukan ma’aikata dubu daya a ma’aikatar ilimi sannan ya amince da daukan wasu ma’aikatan a fannoni daban-daban.
“A bangaren harkar noma ma, gwamnan ya amince da daukan ma’aikatan domin magance matsalar da ake fama da shi na karancin malaman gona.”
“Tun lokacin da gwamnan ya yi alkawari a wajen jawabinsa na rantsuwa, ga shi ba da jimawa ba har ya amince da daukan ma’aikatan, kuma nan ba da jimawa ba ma zai sake daukan wasu. Wannan abun yabawa ne matuka da masa jinjina.”
Daga nan sai ya gargadi masu bukatar aiki da cewa su sanya lura kada wani ko wasu su zo musu da cewa su basu wani abu domin samar musu da aikin yi, “Don Allah a taimakemu duk wanda ya ce a ba shi sisi don ya samar ma wani da aikin yi, to a yi gaggawar zuwa domin samar mana, mu kuma za mu dauki mataki kan kowaye,” ya shaida.
Shugaban ma’aikatan ya bada jerin sabbin ma’aikatan da gwamnan ya dauka da cewa ma’aikatar ilimi ta samu sabbin ma’aikata 1,000; ma’aikatar aikin gona 44; ma’aikatar bunkasa aikin gona (BSADP) 206; ma’aikatar samar da kayan noma da rarrabashi (BASADA) ta samu sabbin jami’ai 90; sai ma’aikatar mata da cigaban yara mai sabbin ma’aikata 70; kwalejin ilimi ta Aminu Saleh, Azare 154; sai kuma kotun daukaka kara ta Shari’a mai sabbin ma’aikata 120.
Daga bisani ya nemi sabbun ma’aikatan da su hada kai da gwamnatin jihar domin ciyar da aiki da jihar Bauchi gaba.