Wata babbar kotu a jihar Oyo da ke zamanta a Ibadan, ta hana ‘yan majalisar dokokin jihar ci gaba da yunkurin tsige mataimakin gwamnan jihar, Rauf Olaniyan.
Kotu karkashin jagorancin mai shari’a Oladiran Akintola, a ranar Laraba, ta umurci ‘yan majalisar da su dakatar da ci gaba da gudanar da bincike kan mataimakin gwamnan.
An rawaito cewa an bukaci Majalisar ta karanta martanin da Olaniyan ya bayar kan zargin da aka yi masa a safiyar Laraba.
Hakan ya faru ne a dai dai lokacin da kotu ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar Talata 5 ga watan Yuli, 2022 domin sauraren karar.
Hakan ya baiwa Majalisar damar mayar da martani kan batutuwan da Mataimakin Gwamnan ya gabatar.
A wani labarin na daban kuma Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da shirin karfafa sojojin Amurka dake NATO a nahiyar Turai, yana mai cewa ana bukatar kawancen adai-dai wannan lokaci fiye da baya.
Yayin taron wani taron ƙawancen ƙasashen Atlantika da ake gudanarwa a Madrid, shugaba Biden yace za’a karfafa NATO ta yadda zata kasance a kowane fanni – ƙasa da Sama da kuma ta ruwa.
Biden, wanda ke ganawa da Sakatare Janar na kungiayar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, ya ce zai yi karin dakarun kasar da su hada da:
Irin matakan da za’a dauka
– Haɓaka rundunar sojojin ruwan Amurka masu aikin wargazau dake Rota na kasar Spaine daga hudu zuwa shida.
– Kafa Hedikwatar Rundanar sojin dindindin ta biyar a Poland.
– “Ƙarin rundunar kai dauki a kasar Romania, wanda ya ƙunshi “dakaru 3,000 da kuma wata karin tawagar ma’aikata 2,000.”
– Sake inganta dakarun sintiri a tekun ƙasashen Baltic.
– Karin wasu tawagogi biyu na jirgin F-35 na sirri zuwa Burtaniya.
– “Ƙarfafa tsaron sararin samani da sauran iyakokin Jamus da Italiya.”
Tunkarar barazana
Da wannan mataki, shugaban Amurka Joe Biden yace tare da kawayen kasar za su tabbatar da cewa NATO a shirye ta ke wajen tunkarar barazanar daga ko wane bangare,”
Yayin da yake ishara da hadin kan kungiyar tsaro ta NATO kan amincewa da bukatar kasashen Finland da Sweden masu tsaka-tsaki a baya na shiga kawancen, Biden ya ce dabarun da Putin ya bi wajen mamaye Ukraine dara ce taci gida.