Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya karɓi baƙuncin sabuwar babbar Sakatariya a gwamnatin tarayya mai wakiltar jihar Zamfara Keshinro.
A Juma’ar nan ne aka bayyana sunan Dr. Maryam Ismaila Keshinro, tare da wasu mutum bakwai a matsayin sabbin manyan sakatarori a ma’aikatun gwamnatin tarayya.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar yau a Gusau, ya bayyana cewa a Lahadin nan ne Gwamna Lawal ya karɓi baƙuncin Dr. Maryam don nuna mata goyon baya da ƙarfafa gwiwa.
Mutanen Da Suka Mutu A Harin Ƙunar Baƙin-Wake A Wajen Bikin Aure Ya Ƙaru Zuwa 18 A Borno
Bayan da ya taya Dr Maryam Murna, Gwamna Dauda Lawal ya hore ta da ta kasance Jakadiyar jihar Zamfara tagari.
“Ina so in yi amfani da wannan dama wajen taya ki murnar kasacewa babbar Sakatariya a gwamnatin tarayya.
“Wannan wata dama ce da mu ke sa rai, tare da yi maki addu’ar amfani da ita wajen yi wa ƙasar nan bauta, tare da bayar da gudumawa wajen sake gina wannan jiha ta mu.
“Gwamnatin jihar Zamfara za ta samar maki da duk irin gudumawar da za ta taimka maki wajen ci gaba, muna alfahari da nasarorin da kika samu a rayuwa.
“Na karɓi baƙuncin ki a yau ne don in nuna maki ƙauna, sannan in sanar da ke cewa muna alfahari da ke a jihar Zamfara.”
A wani labarin na daban gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ya yi alƙawarin gudanar da bincike a kan zargin cirar kuɗaɗen garatuti na ‘yan fansho ba bisa ƙa’ida ba a gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje.
A yayin ƙaddamar da kashi na biyu na biyan kuɗin ƴan fansho na garatuti da na waɗanda suka mutu wanda ya kai har Naira biliyan ₦5b ga kusan ma’aikata 4,000 da suka yi ritaya, gwamnan ya ce sun gano rashin bayanan kuɗaɗen fansho da aka cire.
Gwamna Yusuf ya buƙaci ƙungiyar ’yan fansho ta ƙasa (NUP) reshen jihar da ta nemi a gudanar da bincike kan kuɗaɗen da suka bata. Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta fara gudanar da cikakken bincike, tare da yin alƙawarin hukunta duk wanda aka samu da hannu wajen karkatar da kuɗaɗen fansho.
Gwamnatin jihar na da burin taimakawa wajen kwato da mayar da kuɗaɗen da aka cire ga waɗanda suka yi ritaya da zarar an kammala bincike.
Gwamna Yusuf ya ƙara da cewa, kashi na farko na biyan kuɗin ya raba Naira biliyan ₦6b ga waɗanda suka ci gajiyar tallafin, inda yanzu adadin ya kai Naira biliyan ₦11b.
DUBA NAN: Kotu Zata Cigaba Da Sauraron Karar Neman Hana Ganduje Bayyana Kansa A Shugaban Jam’iyyar APC
Ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na tabbatar da cewa ma’aikatan da suka yi ritaya da kuma iyalan ma’aikatan da suka rasu sun samu haƙƙoƙin su.