Gwamnatin Kamaru ta yi watsi da rahotannin da ke cewa tana ganawa da hukumar kwallon kafar Afirka CAF dangane da yiwuwar janyewa daga karbar bakuncin gasar cin kofin kasashen Afirka ta AFCON, saboda barkewar sabon nau’in cutar Korona na Omicron a sassan kasar.
Dangane da barazanar da kungiyoyin kwallon kafa na nahiyar Turai ke yi kuwa na hana ‘yan wasa zuwa wakilcin kasashensu a gasar ta cin kofin Afirka saboda yaduwar cutar Korona, Minsip ya bayyana matakin a matsayin mugunta tsaba, ta hanyar kafa hujja da bayanai marasa tushe ballantana makama.
A halin da ake ciki, tsanantar sabon nau’in cutar Korona na Omicron ya janyo samun karuwar kungiyoyin Firimiya da ke neman a dage musu wasanninsu zuwa cikin sabuwar shekara ta 2022.
A wani labarin na daban ranar Talata hukumar kwallon kafar Afrika ke shirin fitar da jadawalin gasar cin kofin nahiyar wanda Kamaru za ta karbi bakonci a wannan karon, gasar da ke kunshe da kasashe 24 wadanda za a rabasu zuwa rukunnai 4 kowanne dauke da kasashe 6-6.
Bayanai na nuna cewa taron fitar da jadawalin gasar da zai gudana a Kamaru zai samu halartar manyan-manyan ‘yan wasan nahiyar ta Afrika ciki har da Samuel Eto da Didier Drogba da Yaya Toure da kuma Jay Jay Okocha.
Za dai a faro gasar daga ranar 9 ga watan Janairun 2022 zuwa 6 ga watan Fabarairu.
Hasashe dai na nuna da yiwuwar Senegal da ke matsayin jagorar kwallon kafa a matsayin da FIFA kan fitar ta shiga rukunin farko tare da mai masaukin baki Kamaru kana Algeria mai rike da kambu da kuma Tunisia baya ga Najeriya da Marocco.
Rukuni na biyu da yiwuwar ya kunshi kasashen Masar Ghana Cote d’Ivoire da Mali da Burkina Faso da kuma Guinea
Rukuni na 3 zai iya kunsar Cape Verde da Gabon da Mauritania da Sierra Leone da zimbabwe da Guinea bissau.
Sai rukuni na 4 da zai iya kunsar Malawi da Sudan da Equatorial Guinea da Habasha da Gambia da kuma tsibirin Comoros.