Shugaban NRC mai kula da harkokin jiragen kasa a Najeriya yace jiragen Kano-Legas sun daina aiki.
Akwai matsalar tsaro a yankunan Kaduna da Minna, don haka aka dakatar da aikin jiragen Haka zalika NRC ta tabbatar da cewa jirgin Warri-Itakpe ba zai rika tsayawa a Ajaokuta ba.
Hukumar NRC mai kula da harkokin jiragen kasa a Najeriya ta dakatar da ayyukan jiragen kasan Legas zuwa Kano da kuma jirgin Ajaokuta.
Tribune ta kawo rahoto a ranar Laraba, 3 ga watan Agusta 2022 cewa NRC ta dauki wannan mataki a madadin gwamnati saboda matsalar rashin tsaro.
Majiyoyi da dama daga hukumar ta NRC sun shaidawa manema labarai cewa an dakatar da aikin jirgin Ajaokuta a dalilin harin da aka kai wa wasu.
A ranar Litinin da ta wuce aka samu ‘yan bindiga sun aukawa fasinjoji a yankin Warri-Itakpe. Haka zalika rashin tsaron ya yi sanadiyyar daina aikin jiragen kasan Legas zuwa Kano.
A dalilin haka aka daina amfani da jiragen Kaduna zuwa Abuja. Rahoton Punch ya nuna ba za a dawo aiki ba har sai lokacin da aka iya tabbatar za a iya kare lafiyar ma’aikata da fasinjojin da ke bi ta wadannan hanyoyi.
Babbar Darektan NRC na kasa, Fidet Okhiria ya tabbatarwa manema labarai cewa jiragen Legas zuwa Kano da na Ajaokuta sun daina aiki a halin yanzu.
Da yake magana game da Warri-Itakpe, Fidet Okhiria ya shaida cewa ba za su dakatar da aiki a hanyar ba, sai dai ba za a rika dakatawa a Ajaokuta ba.
“Dalili kuwa shi ne a jiya (Litinin), yayin da wasu fasinjoji suke barin tashar jirgi a motocinsu, sai aka samu mutane sun buda masu wuta.
Saboda haka sai muka ce ba za mu sake tsayawa a nan ba (tashar Ajaokuta) saboda fasinjoji.” – Fidet Okhiria.
Akwai matsala a hanyar Kaduna/Neja A bayanin da yayi a ranar Talata, shugaban NRC yace jirgin Warri-Itakpe yana aiki, amma babu maganar a tsaya a Ajaokuta saboda halin da ake ciki a yau.
Baya ga jirgin Legas zuwa Kano, babu wani jirgin kasa da ba ya aiki.
Dalilin dakatar da aikin jiragen shi ne matsalar rashin tsaro a yankin Minna da Kaduna.
Tare jirgin Kaduna – Abuja A watan Maris ku ka samu labari Rotimi Amaechi, a lokacin yana Ministan sufuri, yace ya yi hasashen harin da aka kai wa jirgin kasan Kaduna-Abuja.
Rotimi Amaechi yace tun farko sai da ya bukaci a kashe N3bn wajen sayan wasu kayan tsaro, rashin tanadar wadannan kayan aiki ya jawo matsalar.
Source:hausalegitng