Batun karin albashi na daya daga cikin bukatun da kungiyar malaman jami’a ke kara tada jijiyar wuya a kai.
Watanni sama da shida kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta yi tana kai ruwa rana da gwamnatin Buhari.
Bincike ya bayyana kudaden da ake biyan lakcarorin da ke karkashin kungiyar ASUU a jami’o’in Najeriya.
Daya daga cikin abubuwan dake damun ASUU kuma ya kai ga yajin aiki shine kawo tsarin biyan albashi na bai daya (IPPIS) tare da ture wanda a baya suke kai UTAS.
A wani bangaren kuma, suna kokawa ne game da yadda gwamnati ke yiwa jami’o’in Najeriya rikon sakainar kashi, musamman duba da alkawarin da gwamnti ta yi na inganta aikin da albashin malamai.
To amma wani hanzari ba gudu ba, wai shin nawa malaman jami’a ke samu? Kuma shin albashin na da kaurin da zai iya rike matsakaicin ma’aikaci a Najeriya?
Lakraca na II – daga N137,459 zuwa N164,970 a kowane wata
Lakcara I – daga N173,333 zuwa N223,667 a kowanne wata
Babban lakcara – daga N257,625 zuwa N371,292 a kowane wata
Makaranci – daga N314,018 zuwa N417,062 a kowane wata
Farfesa – daga N381,695 zuwa N501,680 a kowane wata
A gefen wata tattaunawa, ministan ilimi, Adamu Adamu, yace gwamnati za ta iya kara wa malaman jami’a albashi da 23.5%, yayin da farfesoshi za su samun karin 35%.
Ministan ya bayyan ahakan ne a yau Talata 6 ga watan Satumba a babban birnin tarayya Abuja yayin tattaunawa da shugabannin jami’o’in gwamnatin tarayya, Punch ta ruwaito.
Ministan ya kuma bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi gargadi game da kulla wasu yarjejeniyoyin da gwamnati ba za ta iya dauka ba.
Mun Yi Duk Mai Yiwuwa Don Ganin Mun Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU, Gwamnatin Buhari.
A wani labarin, bayan da aka shafe watanni ana kai ruwa rana a batun yajin aikin ASUU, gwamnatin Buhari a ranar Talata ta ce ta yi iyakar kokarinta don ganin ta kawo karshen rikicin gwamnati da kungiyar malaman jami’o’i.
Wannan na fitowa ne daga bakin ministan ilimi, Adamu Adamu a wata ganawa da ake yi da shugabannin jami’o’in tarayya da hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) a Abuja.
Ya zuwa yanzu dai da rahoton nan ke shigowa mana daga jaridar The Nation, an ce manyan jami’an na gwamnati suna cikin ganawar sirri.
Source: LEGITHAUSA