Jami’an tsaro na yin ganawar sirri da gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da Sarki Sanusi II a fadar Sarkin Kano.
Wannan dai na zuwa ne bayan da Aminu Ado Bayero ya dawo jihar da zummar komawa kan kujerar masarautar Kano.
Hakan ya haifar da tashe-tashen hankula, lamarin da ya sanya aka jibge jami’an tsaro a fadin jihar.
A wata hira ta faifan bidiyo da aka yi da shi a fadar Sarkin Kano da ke Gidan Rumfa a yau Asabar, mataimakin gwamnan ya yi iƙirarin cewa hukumar NSA ce ta bayar da jiragen sama guda biyu domin jigilar hamɓararren Sarki Aminu Ado Bayero zuwa Kano.
Aminu Ado, wanda ya kai ziyarar gani da ido Awujale na Ijebuland a jihar Ogun, ya dawo Kano da sanyin safiyar yau Asabar in da ya koma wata ƙaramar tsohuwar fada da ke Nassarawa.
Hakan ya saɓa da korarsa da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi bayan tsige shi tare da ƙarin wasu Sarakunan da tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya naɗa. Gwamnan ya ba tsigaggun Sarakunan sa’o’i 48 da su bar fadarsu tare da mika su ga kwamishinan kananan hukumomi da masarautu.
Duba Nan: Majalisar Dokokin Kano Za Ta Yiwa Dokar Masarautun Kano Gyaran Fuska
Tuni gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin kama Sarki Aminu Ado saboda a cewarsa zuwan nasa zai iya kawo hargitsi a jihar. Sai dai rahotanni sun bayyana cewa akwai tarin jami’a an tsaro a ƙaramar fadar da shi Sarki Aminu ya sauka.