Ministan harkokin cikin gida na kasar Irak Abdul Amir Al-Shammari ya jaddada halartar sama da jami’an tsaro 40,000 wajen tabbatar da aikin tarin Arba’in a Karbala.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – ya habarta cewa, Ministan harkokin cikin gida na kasar Iraki Abdul Amir Al-Shammari ya ce a farkon makon nan ne za a fara shirin jigilar maziyartan tare da halartar jami’an tsaro 40,000 na sojoji da ‘yan sanda da kuma al-Hashd al-Shaabi don kare masu taron.
Al-Shammari ya kara da cewa lardin Diyala na daya daga cikin wuraren da ake fara yunkurin zuwa Karbala, kuma yana da muhimmanci saboda kasancewar mashigar Al-Manzariyeh tare da kasar Iran da kuma yawan zuwan Maziyartan daga kasar Iran, wanda ke kai mutane 50,000 a kowace rana.
Source: LeadershipHausa