Sunday Igboho ya maka gwamnatin tarayya a kotu bisa yin kutse a gidansa inda yake bukatar naira biliyan 5.5 Jami’an hukumar DSS sun kutsa gidan Igboho dake Ibadan a ranar 1 ga watan Yuli inda har aka kashe mutane 2 kuma aka kama mutane 12.
Dama an kama Igboho da matarsa ne a babban filin jirgi sama dake Cotonou a ranar Litinin sannan aka gabatar dashi a gaban alkali Sunday Adeyemo, mai rajin kwatar kasar Yarabawa wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya maka gwamnatin tarayya a kotu bisa kutsa mishi gida inda yake bukatar a biya shi naira biliyan 5.5. .
Jami’an hukumar DSS sun kutsa gidan Igboho dake Ibadan a ranar 1 ga watan Yuli. Sakamakon hakan an kashe mutane 2 kuma an kama mutane 12 lokacinJami’an hukumar DSS sun kutsa gidan Igboho dake Ibadan a ranar 1 ga watan Yuli. Sakamakon hakan an kashe mutane 2 kuma an kama mutane 12 lokacin.
Kamar yadda TheCable ta ruwaito, Igboho ya ce yana cikin gidan shi a lokacin amma jami’an DSS basu gan shi ba.
Igboho ya maka FG a kotu, yana bukatar N5.5bn na diyyar kutse a gidansa.
Saidai an kama shi a babban tashar jirgin sama dake Cotonou a jamhuriyar Benin a ranar Litinin. An gabatar dashi a gaban alkali a Cour De’appal De Cotonou.
Lauyansa , Yomi Aliyu, ya gabatar da bukatar masu rajin kare hakkin bil’adama a babbar kotun dake Ibadan inda yake bukatar ga gwamnatin tarayya.
Ya hada har da Antoni janar da hukumar DSS a korafin nasa, ChannelsTV ta ruwaito. Kamar yadda ya gabatar da korafin: “Sakamakon kutse da lalata masa dukiya a gidansa da misalin 1am zuwa 3am wanda hakan ya yi karantsaye akan hakkin bil’adama kuma wajibi ne gidansa ya samu kariya bisa kundin tsarin mulkin Najeriya, bangare na 37, 43 da 44 na 1999 .
“Sannan hukumar ta dakatar da Igboho daga nema wa Yarabawa hakkinsu inda tayi ta kai masa farmaki da bindiga don nemansa a raye ko a mace duk da cewa mutum ne shi mai neman zaman lafiya. “
”Sakamakon haka yana rokon kotu mai alfarma da ta umarci gwamnatin tarayya ta biya shi naira biliyan 5 akan shiga hakkinsa.” Sannan takarda ta bukaci wadanda ake kara da su bayar da hakuri sakamakon cutar da Igboho da suka yi.
A wani labari na daban, fadar shugaban kasa ta yi ikirarin cewa ba a rasa rai ko daya ba kuma babu bam ko daya da ya tashi yayin bikin babbar sallah balle a kai ga harin ‘yan bindiga ko na ‘yan ta’adda.
Femi Adesina, mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da hakan a wata wallafa da yayi a shafinsa na Facebook mai taken “Ubangiji ya albarkaci dakarunmu.”